Sanata Ya Faɗawa Hausawa Kiristoci Amfanin Zaɓen Tinubu a 2027
- Sanata Sunday Katung ya bukaci Kiristocin Hausawa da ke Kaduna su goyi bayan sake zaben Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani a 2027
- Katung ya ce lokacin siyasar rarrabuwar kawuna ya wuce a Kaduna, yana mai cewa gwamnatocin APC sun himmatu wajen tabbatar da adalci
- Ya kuma bukaci al'ummar Kiristocin Hausawa su taimaka wajen wayar da kan masu kada kuri'a a rumfunan zabe, kananan hukumomi da mazabu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Sanata mai wakiltar Kaduna ta Kudu, Sunday Katung, ya bukaci Kiristocin Hausawa da ke jihar Kaduna su marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani baya domin sake zabensu a 2027.
Katung ya yi wannan kira ne a ranar Alhamis, 12 ga watan Nuwamba, yayin wani taron tattaunawa da ya gudanar da mambobin kungiyar Kiristocin Hausawa a mazabar Kaduna ta Arewa, da ke Zariya.

Source: Twitter
Sanata ya yi Hausawa Kiristoci hakuri
Kakakinsa, Joseph Midat, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, cewar rahoton Vanguard.
Sanatan ya bayyana cewa siyasar rarrabuwar kawuna ta zama tarihi a Kaduna, yana mai cewa gwamnatocin Tinubu da Uba Sani sun nuna aniyarsu ta tafiyar da mulki ba tare da nuna wariya ga wani bangare na al'umma ba.
Ya ce adalci, gaskiya da hada kan jama'a za su ci gaba da kasancewa ginshikan manufofin 'yan takarar APC, inda ya bukaci matasa su kasance masu zaman lafiya da hadin kai tare da taka rawa a harkokin siyasa.
Katung ya kara da cewa babu wani shiri na raba kan al'umma ko nuna bambanci, domin siyasar da ake bukata a yanzu ita ce wadda za ta mayar da hankali kan ci gaba da hada kan jama'a.
Ya yi alkawarin samar da ayyukan ci gaba
Sanatan ya bayyana yawan matasa a matsayin wata muhimmiyar dama ga APC wajen samun goyon bayan masu kada kuri'a a zaben 2027, cewar Punch.
Ya kuma yi alkawarin ci gaba da kare muradun matasa tare da hada kai da sauran shugabannin siyasa domin jawo ayyukan raya kasa, mukamai da damarmakin tattalin arziki zuwa yankunansu.
Katung ya bukaci Kiristocin Hausawa su rungumi shirin siyasar APC ta hanyar wayar da kan jama'a da neman goyon baya a rumfunan zabe, mazabu da kananan hukumomi.
Ya ce zaben 2027 wata dama ce ga al'ummar Kaduna wajen nuna kudurinsu na zaman lafiya, hadin kai, ci gaba da kuma ci gaba da manufofin gwamnatin APC.

Source: Facebook
Abin da mataimakin gwamnan ya ce
Da yake jawabi a wurin taron, Jerry Adams, wanda ke takarar mataimakin gwamnan Kaduna tare da Uba Sani a 2027, ya yabawa Katung bisa shirya taron.
Adams ya kuma gode wa masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suke bai wa jam'iyyar APC.
Ya bayyana wasu ayyukan da gwamnatocin tarayya da jiha suka aiwatar a Kaduna, ciki har da kafa cibiyoyin gwamnatin tarayya da cibiyoyin koyar da sana'o'i a dukkan shiyyoyin sanatan jihar guda uku.
Tinubu ya yi maraba yan Kudancin Kaduna
A wani labarin, an ji cewa shugaba Bola Tinubu ya karbi manyan jiga-jigan siyasar Kudancin Kaduna da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Tinubu ya bayyana cewa sauya shekar da manyan yan siyasa ke yi zuwa APC na nuna yadda jam'iyyar ke kara karbuwa a wurin jama'a.
Masu sauya shekar, ciki har da yan Majalisa sun ce nasarorin Tinubu da Gwamna Uba Sani ne suka jawo hankalinsu zuwa APC.
Asali: Legit.ng


