Yadda wasu mutane 8 su ka kashe tare da sayar da kokon kan mutane 31

Yadda wasu mutane 8 su ka kashe tare da sayar da kokon kan mutane 31

- Hukumar 'yan sanda ta yi bajakolin wasu mutane 8 bisa zarginsu da satar mutane, kisa, tsafi da kuma cinikayyar sassan jikin mutane

- Jami'an 'yan sanda sun yi nasarar samun sassan jikin mutane da su ka hada da kasusuwa, gashi, kokon kan mutane da sauran su bayan birkice gidan wani mutum mai suna Azeez

- Masu laifin sun ce su na sayar da kowanne kokon kan mutum a kan Naira N15,000 ga kwastomominsu

Hukumar 'yan sanda ta yi bajakolin wasu mutane 8 bisa zarginsu da satar mutane, kisa, tsafi da kuma cinikayyar sassan jikin mutane a garin Ilorin, jihar Kwara.

Wadanda ake zargin, kamar yadda hukumar 'yan sanda ta sanar, sun amsa laifin sayar da kokon kan mutane 31 ga wasu mutane a Ilorin da jihar Kwara.

Wadanda ake zargin su ne; Yakub (Baba Muri), Abdulrazaq Babamale, Aishat Yunisa, Lukman Saka, Ahmed Yahaya (Eko), Abdulfatai Kadri (Adedoyin), kwamandan 'yan sintiri na Ilorin, Adeta Zone, Soliu Ayinde da Abdulganiyu Bamidele.

Yadda wasu mutane 8 su ka kashe tare da sayar da kokon kan mutane 31
Yadda wasu mutane 8 su ka kashe tare da sayar da kokon kan mutane 31
Asali: Twitter

Da yake gabatar da masu laifin, kakakin hukumar 'yan sanda na kasa, Jimoh Moshood, ya bayyana cewar shugaban rundunar 'yan sanda ta kasa, Ibrahim K. Idris, ne ya tura runduna ta musamman jihar Kwara bayan yawaitar korafin satar mutane, tone kabari da kisan mutane domin yin tsafi da sassan jikinsu.

Moshood ya bayyana cewar sun yi nasarar kama masu aikata miyagun laifukan ne ta hanyar samun sahalewar kotu domin binciken gidan wani mai suna Azeez Yakub da ke garin Ilorin bayan samun wasu bayanan sirri.

DUBA WANNAN: Jaridar Naij.co.m ta bayyana dalilin canja suna zuwa Legit.ng

Jami'an 'yan sanda sun yi nasarar samun sassan jikin mutane da su ka hada da kasusuwa, gashi, kokon kan mutane da sauran su bayan birkice gidan.

Bayan tsananta bincike ne jami'an 'yan sandan na hadin gwuiwa su ka gano ragowar mutane 7 da ke aiki tare da Azeez.

Masu laifin sun ce su na sayar da kowanne kokon kan mutum a kan Naira N15,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng