Dumu-dumu: Dattijo ya mutu a dakin karuwa

Dumu-dumu: Dattijo ya mutu a dakin karuwa

- An tsinci gawar wani mutum mai shekaru 40 a wani gidan karuwai da ke Port Harcourt

- Dan uwan mamacin ya ce suna zargin akwai lauje cikin nadi a batun mutuwar

- A cewarsa, sai da ya mutu da wasu sa'o'i tukunna aka sanar musu da mutuwarsa

An tsinci gawar wani Enuduisu Godday Odili, mai shekaru 40 a gidan wasu karuwai da ke layin Azikwe Mile 2, Diobu, PortHarcourt, jihar Rivers, Daily Trust ta wallafa.

Dan uwan mamacin, Chukwuemeka Odili ya tabbatar wa manema labarai a Port Harcourt, inda yace mamacin dan asalin jihar Delta ne, ya sauka a dakin wata karuwa a ranar Alhamis amma an tsinci gawarsa washegari.

Chukwuemeka Odili ya bukaci a yi bincike mai tsanani don a gano asalin abinda ya kashe dan uwansa.

A cewarsa, sai da ya mutu da wasu sa'o'i tukunna aka sanar da su, shiyasa suke zargin akwai lauje cikin nadi.

KU KARANTA: Hotunan ranar daurin auren jarumi Nuhu Abdullahi da zukekiyar amaryarsa

Dumu-dumu: Dattijo ya mutu a dakin karuwa
Dumu-dumu: Dattijo ya mutu a dakin karuwa. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Gagarumin rikici ya barke bayan 'yan daba sun fada kotu tare da fatattakar alkali da lauyoyi

A wani labari na daban, Ishaku Elisha Abbo, Sanata mai wakiltar mazabar Adamawa ta arewa ya tsallake rijiya da baya.

Kamar yadda Legit.ng ta ga wata takarda wacce tazo daga ofishin yada labaran sanatan, wani mutum mai dauke da bindigar toka ya lallabo ya tare shi, inda yayi barazanar harbinsa matsawar bai bashi miliyan 2 ba.

Takardar, wacce hadimin sanatan a kan harkokin yada labarai, Michael Volgent ya saka hannu, ya ce al'amarin ya faru ne da misalin 2pm, inda matasa da yawa suka tare hanyar, yana hanyarsa ta zuwa bikin dan uwansa da ke Mubi.

Kowa ya san sanata Abbo a matsayinsa na mutum mai taimako.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel