An Fitar da Bidiyon Seyi Tinubu yayin da Ya Je Fadar Sarkin Musulmi

An Fitar da Bidiyon Seyi Tinubu yayin da Ya Je Fadar Sarkin Musulmi

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya samu bakuncin ɗan Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, Seyi Tinubu, a fadarsa da ke Sokoto.
  • Seyi Tinubu, wanda shi ne jagoran ƙungiyar Nigeria City Boy Movement, ya kai ziyarar tare da tawagarsa da wasu shugabannin ƙungiyar
  • Ziyarar ta ba su damar gaisawa da Sarkin Musulmi, wanda ya jaddada muhimmancin haɗin kai, fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin ’yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto – Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya samu ziyarar ban girma daga wajen Seyi Tinubu, ɗan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a fadarsa da ke jihar Sokoto.

Seyi Tinubu, wanda shi ne jagoran ƙungiyar Nigeria City Boy Movement, ya kai ziyarar ne a wani ɓangare na ayyukan da yake gudanarwa a jihar Sakkwato.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana da ɗansa Seyi ya samu babbar sarauta a Kebbi

Sarkin Musulmi da Seyi Tinubu
Lokacin da Seyi Tinubu ya ziyarci Sultan a Sokoto. Hoto: City Boy Movement
Source: Facebook

Kungiyar City Boy da ke kula da jihohin Arewa ta Yamma ta wallafa bidiyon ziyarar dan shugaban kasar a wani sako da ta fitar a shafinta na X.

Tawagar da ta raka shi ta haɗa da shugabannin ƙungiyar na ƙasa da kuma mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Hon. Abdulazeez Abubakar Kaka, wanda aka fi sani da Abunaah.

Seyi Tinubu ya kai gaisuwa ga Sultan

Ziyarar ta ba Seyi Tinubu da tawagarsa damar gaisawa da Sarkin Musulmi tare da nuna girmamawa ga masarautar Sokoto.

A yayin karɓar tawagar, Sarkin Musulmi ya nuna jin daɗinsa kan ziyarar, tare da jaddada muhimmancin fahimtar juna da mutunta juna tsakanin al’ummar Najeriya.

Ya kuma bayyana muhimmancin haɗin kai da tattaunawa wajen samar da zaman lafiya da bunƙasa ƙasa.

Makasudin ziyarar Seyi wajen Sultan

An bayyana cewa ziyarar ta kuma nuna irin rawar da cibiyoyin sarakunan gargajiya ke takawa wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa da samar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Iran ta fitar da bidiyon rumbun makamai da ke karkashin kasa

Sarkin Musulmi ya jaddada muhimmancin tattaunawa da kyakkyawar mu’amala tsakanin sassa daban-daban na al’umma domin tabbatar da zaman tare.

Haka kuma, ziyarar ta nuna yadda shugabancin gargajiya ke ci gaba da taka rawa wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin al’umma da tallafa wa ci gaban ƙasa.

Sarkin Musulmi a wajen taro
Mai alfarma Sarkin Musulmi na bayani a wajen taro. Hoto: JNI
Source: Facebook

Ana ganin cewa ziyarar na da alaka da yadda dan shugaban kasar ke ziyartar wurare domin nemawa mahaifinsa goyon baya a zaben 2027.

Sa dai babu wani rahoto da ya nuna cewa an yi maganar siyasa ko neman goyon shugaba Bola Tinubu a ziyarar da Seyi ya kai.

An shiga Jumada II a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya sanar da cewa Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026, ita ce ranar farko ta watan Jimada Sani na shekarar 1448 bayan hijira.

Sanarwar fadar Sarkin Musulmi ta bayyana cewa ba a samu rahoton ganin jinjirin watan Jimada Sani daga kwamitocin duban wata a sassan Najeriya ba a ranar Litinin, 9 ga Nuwamba.

Saboda haka, fadar ta ayyana Talata, 10 ga Nuwamba, a matsayin ranar cika kwana 30 na watan Jimadal Ula, yayin da Laraba ta zama farkon watan Jimada Sani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng