Yan Wasan Kwaikwayo Sun Gane Siyasa, Jarumi Zai Nemi Takarar Majalisar Tarayya
- Shahararren jarumin Nollywood, Olumide Oworu, ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar majalisar wakilai mai wakiltar Surulere I a jihar Lagos
- Jarumin mai shekaru 31 ya ce kalubalen da ya fuskanta a zaɓen 2023 bai karya masa gwiwa ba, kuma yana son shiga harkokin shugabanci
- Oworu zai sake neman kujerar siyasa ne a ƙarƙashin jam’iyyar APM, bayan ya sauya sheƙa daga jam’iyyar Labour Party da ya yi amfani da ita a 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos — Shahararren jarumin fina-finan Nollywood, Olumide Oworu, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai.
Dan wasan kwaikwayon zai nemi takarar ne daga mazabar Surulere I a jihar Lagos a zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara.

Source: Instagram
Jarumin ya sanar da matakin ne a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamba, 2026, ta wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Jam'iyyar da matashin zai tsaya
Ya bayyana hoton kamfen ɗinsa a ƙarƙashin jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) a cikin wani bidiyo da ya wallafa.
Oworu, mai shekaru 31, ya bayyana manufar takararsa da taken “Reset Nigeria”, wato sake fasalin Najeriya.
Ya ce abin da ya faru da shi a zaɓen 2023 ya ƙara masa ƙwarin gwiwar shiga harkokin shugabanci, duk da matsalolin gudanarwa da suka hana sunansa bayyana a takardar zaɓe ta ƙarshe.
A kalamansa:
“ A shekarar 2023, mun yi ƙarfin halin yin imanin cewa abubuwa za su iya sauyawa. Mun fito, mun shirya kanmu, kuma mun tabbatar da cewa matasan mazabar Surulere 1 a shirye suke su samu shugabanci mai tafiya bisa lamiri.”
Jarumin ya ƙara da cewa abin da ya faru a wancan lokacin bai raunana ƙudurin magoya bayansa ba, domin juriyarsu ta nuna cewa burinsu ba wani abu ne da zai wuce na ɗan lokaci ba.

Source: Instagram
Ya buƙaci matasa su shiga siyasa
Haka kuma, Oworu ya yi kira ga matasan Najeriya da su ƙara shiga harkokin siyasa, yana mai gargaɗin cewa ba za su iya ci gaba da zama a gefe ba yayin da shugabanni ke yanke shawarar da za ta shafi makomarsu.
Sanarwar takararsa ta nuna komawarsa harkokin neman zaɓe, bayan yunƙurinsa na farko a shekarar 2023, lokacin da ya nemi kujerar majalisar dokokin jihar Lagos mai wakiltar Surulere I a ƙarƙashin jam’iyyar Labour.
A wancan lokacin, ana sa ran zai fafata da ɗan majalisar da ke kan kujerar, Desmond Elliot, wanda shi ma jarumin fina-finai ne.
Sai dai sunan Oworu bai bayyana a takardar zaɓe ta ƙarshe ba, yayin da aka sanya sunan Adebayo Bode a matsayin ɗan takarar Labour a sakamakon zaɓen hukumance.
Jarumin Kannywood ya taba shiga takara
A baya, an ji cewa jarumin Kannywood, Lawan Ahmad, ya tabbatar da shiga tseren takarar mamba mai wakiltar Bakori a majalisar dokokin Katsina.
Jarumin wanda tauraruwarsa ke haskawa a shirin Izzar So da sunan Umar Hashim, ya fito siyasar ne karkashin jam'iyyar APC.
Ahmad ya roki mutane su taya shi da addu'a kan lamarin, sannan su yi gum da bakin su matukar ba alheri za su faɗa ba.
Asali: Legit.ng


