Kotu Ta bada Umarnin Aiwatar da Hukuncin da Aka Yanke Wa Dan Abdulrasheed Maina

Kotu Ta bada Umarnin Aiwatar da Hukuncin da Aka Yanke Wa Dan Abdulrasheed Maina

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare Faisal, ɗan tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho, Abdulrasheed Maina, a gidan yari
  • Kotun ta umarci tsare Faisal a gidan gyaran hali ne domin ya fara zaman hukuncin da aka yanke masana na shekaru bak
  • Mai shari’a James Omotosho ns ya bayar da umarnin ne bayan Hukumar EFCC ta shigar da ƙara ta musamman domin a aiwatar da hukuncin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin a tsare Faisal, ɗan tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho, Abdulrasheed Maina, a gidan gyaran hali.

Kotun ta bada umarnin a tasa Faisal zuwa gidan gyaran hali domin ya fara zaman hukuncin ɗaurin shekaru bakwai da aka yanke masa tun farko.

Kara karanta wannan

Za a mika dan Najeriya zuwa Amurka Trump su yi masa hukunci

Faisal.
Faisal, dan tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho, Abdulrasheed Maina Hoto: I-G Musa
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa mai shari’a James Omotosho ne ya bayar da umarnin bayan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta shigar da bukatar hakan.

An sake kama Faisal ne a ranar 14 ga Oktoba, sannan Hukumar DSS ta miƙa shi ga EFCC bayan ya tsere daga beli tare da ƙin halartar shari’arsa kimanin shekaru shida da suka gabata.

Yadda shari’ar Faisal ta kaya

An gurfanar da Faisal a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a shekarar 2019 kan tuhume-tuhume uku da suka shafi halatta kuɗaɗen haram da kuma rashin bayyana cikakkun bayanai a fom ɗin bayyana kadarori.

Bayan ya musanta tuhume-tuhumen da aka gabatar masa a gaban Mai shari’a Okon Abang, wanda yanzu yake alƙalin Kotun Ɗaukaka Ƙara, Faisal ya tsere daga beli tare da kauce wa shari’ar.

Hakan ya sa Mai shari’a Abang ya ci gaba da sauraron shari’ar ba tare da Faisal ya halarta ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun je har gida sun harbe shugaban Miyetti Allah

A ranar 7 ga Oktoba, 2021, alƙalin ya yanke hukunci inda aka same shi da laifi, sannan aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyar kan tuhume-tuhume na ɗaya da na uku, yayin da aka yanke masa shekaru 14 kan tuhuma ta biyu.

Alƙalin ya bayar da umarnin cewa hukuncin kan dukkan tuhume-tuhumen zai gudana ne lokaci guda. Ya kuma umarci a kama Faisal a duk inda aka same shi, a kai shi gidan gyaran hali domin ya fara zaman hukuncin.

EFCC ta nemi aiwatar da hukuncin

Bayan sake kama Faisal, EFCC ta shigar da ƙara ta musamman tana neman izinin kotu domin ta nemi aiwatar da hukuncin da Mai shari’a Abang ya yanke a ranar 7 ga Oktoba, 2021.

Ta ce ya kamata a fara ƙirga zaman hukuncin daga ranar 14 ga Oktoba, 2026, wato ranar da aka sake kama shi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Bayan gabatar da buƙatar, Mai shari’a Omotosho ya amince da ita. Alƙalin ya ba EFCC izinin neman aiwatar da hukuncin.

Kotu.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita yayin zaman kotu Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Omotosho ya bayyana cewa bisa ga hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na ranar 24 ga Nuwamba, 2022, hukuncin da Faisal zai yi shi ne shekaru uku a kan tuhuma ta ɗaya, shekaru bakwai a kan tuhuma ta biyu, da shekaru uku a kan tuhuma ta uku.

Kara karanta wannan

Shugaban INEC ba ya son a fitar da takardun Tinubu, ya shigar da bukata gaban kotu

Ya ce za a gudanar da dukkan hukuncin ne lokaci guda, daga ranar 14 ga Oktoba, wato ranar da aka sake kama Faisal.

EFCC na neman mahaifin Faisal

Kun ji cewa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ƙaddamar da neman tsohon shugaban kwamitin gyaran tsarin fansho, Abdulrashid Maina.

Hukumar ta bukaci hukumomin tsaro, ciki har da Hukumar Shige da Fice, su zauna cikin shirin ko-ta-kwana domin kama Maina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262