Ana Zargin N78bn na Kuɗaɗen Tallafin Jama'a Sun Yi Ɓatan Dabo a gwamnatin Tinubu

Ana Zargin N78bn na Kuɗaɗen Tallafin Jama'a Sun Yi Ɓatan Dabo a gwamnatin Tinubu

  • Kungiyar SERAP ta bukaci Bola Tinubu ya binciki zargin karkatar da sama da N78.8bn na kudaden tallafin kudi a gwamnatinsa
  • Kungiyar ta ce NCTO ta kasa gabatar da bayanan REMITA da za su tabbatar da biyan N33.751bn ga gidaje da masu cin gajiyar shirin
  • SERAP ta bukaci a binciki kudaden da ba a yi wa binciken biyan kudi ba, tare da dawo da dukkan kudaden gwamnati da aka kashe ba bisa ka’ida ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyar kare hakkin jama’a da tabbatar da gaskiya a harkokin tattalin arziki, SERAP, ta bukaci binciken gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kungiyar ta bukaci Tinubu ya dauki matakin gaggawa kan zargin almundahanar kudaden gwamnati na tallafi da yake bayarwa.

SERAP ta bukaci Tinubu ya binciki baran N78bn na tallafi
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da SERAP ke yawan tuhuma a kasar. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Twitter

Abin da SERAP ke bukata daga Tinubu

Kara karanta wannan

"Ka yi yadda na yi," Atiku ya sake kinkimo magana mai girma kan bayanan Tinubu na Amurka

SERAP ta bukaci Tinubu ya umarci Ma’aikatar Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, NCTO da NASSCO su yi bayani kan sama da N78.8bn da ake zargin an karkatar, kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.

Zargin ya bayyana ne a cikin rahoton shekara na 2024 da Babban Mai binciken Kudi na Tarayya ya wallafa ranar 7 ga Agusta, 2026.

A cewar rahoton, binciken ya shafi lokuta daban-daban daga Janairu zuwa Disamba 2023, da kuma wasu bayanai da suka kare ranar 31 ga Disamba, 2024.

SERAP ta bukaci Shugaban kasa ya umarci Ma’aikatar da NCTO su wallafa cikakkun bayanan N33.751bn da aka kashe wajen biyan tallafin tsabar kudi a 2023.

Kungiyar ta ce bayanan ya kamata su kunshi sunayen wadanda suka amfana, kudaden da aka biya, tantancewa, izini da kuma yadda aka daidaita bayanan kudaden.

Ana zargin bayan N78bn na tallafi a gwamnatin Tinubu
Shugaba Bola Tinubu yana duba takardu a ofishinsa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Zarge-zargen da SERAP ke yi wa Tinubu

SERAP ta bukaci Tinubu ya umarci Ma’aikatar da NCTO su yi bayanin N36.744bn da aka biya ba tare da gudanar da binciken kudi kafin biyan ba.

Ta kuma bukaci a yi bayani kan N4.616bn na kashe-kashen da ba su da isassun takardun shaida, N350.182m na rajistar masu cin gajiyar shirin da N89.511m na kayan ajiya.

Kara karanta wannan

Ma’aikata sun yanke sabon mafi karin albashin da suke so ganin N70000 ta yi kadan

Haka kuma, kungiyar ta bukaci a yi bayanin N17.422m da aka bayar a matsayin kudin sayen dizal, tare da gano yadda aka kashe wadannan kudade.

SERAP ta kuma bukaci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa su gudanar da cikakken bincike kan N76.24bn na kudaden NCTO da ake zargi ba a yi bayani a kansu ba.

Kungiyar ta ce ya kamata a kuma binciki N2.55bn na kudaden NASSCO, tare da dawo da duk wani kudin gwamnati da aka kashe ko karkatar da shi ba bisa ka’ida ba.

Ta bai wa gwamnati kwanaki bakwai daga lokacin da ta karbi ko aka wallafa wasikar domin daukar matakan da ta bukata.

SERAP ta yi gargadin cewa idan ba ta samu amsa cikin kwanaki bakwai ba, za ta yi la’akari da daukar matakin shari’a, ciki har da kai karar zuwa Kotun ECOWAS.

SERAP ta kai karar Tinunu kan ta'addanci

An ji cewa kungiyar SERAP ta bukaci Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi amfani da Mataki na 99 domin kai Najeriya Kwamitin Tsaro.

Rahoton ya nuna yadda sace-sacen mutane da kashe-kashe ke ƙaruwa a jihohin Oyo, Benue, Borno da sauran sassan Najeriya tare barazana ga fararen hula.

SERAP ta nemi Majalisar ta sa ido kan Najeriya ta gudanar da bincike kare fararen hula da tabbatar da hukunta masu aikata laifi gaggawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.