Aikin Mambilla ya dawo baya: Kamfani ya tafi kotun Duniya, ya nemi Najeriya ta yi kashin N200bn

Aikin Mambilla ya dawo baya: Kamfani ya tafi kotun Duniya, ya nemi Najeriya ta yi kashin N200bn

- Sunrise Power Transmission Company of Nigeria ta kai karar Gwamnatin Tarayya

- Kamfanin ya bukaci a biya shi kudi saboda saba yarjejeniyar da aka yi da shi a baya

- Femi Falana ya tsayawa SPTCL, ya bukaci Gwamnati ta biya kamfanin fam $400m

Kamfanin Sunrise Power Transmission Company of Nigeria Ltd watau SPTCL ya na yunkurin kawo cikas a aikin samar da wutar lantarkin Mambilla.

Daily Trust ta ce kamfanin ya shirya kai karar gwamnatin tarayya ya na neman a biya shi $400m ya rage zafi saboda an sabawa yarjejeniyar da aka yi da shi.

Kamar yadda takardun shigar da karar suka bayyana, wannan kamfanin ya dumfari babban kotun kasuwancin Duniya da ke birnin Faris, kasar Faransa.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya za ta sayo makaman N770bn saboda matsalar tsaro

Sunrise Power Transmission Company of Nigeria ya ce gwamnatin tarayya ya ki cika alkawarin da aka yi tun 2020 na cewa za a biya shi fam Dala miliyan 200.

Kamfanin na SPTCL ya ce bai kamata a wuce watanni shida ba a biya shi wadannan hakkokinsa ba. Ita kuma gwamnati ta na kukan karancin kudi a halin yanzu.

Lauyan da ya tsayawa kamfanin a kotun Duniya shi ne Femi Falana, wanda ya rubuta takarda ya na bukatar a ci gwamnatin Najeriya tara na Dala miliyan 400.

Kamfanin ya yi ikirarin cewa tun 2003 ya kawo maganar kwangilar Mambilla a jihar Taraba domin gwamnatin tarayya ta inganta sha’anin wutar lantarki.

Aikin Mambilla ya dawo baya: Kamfani ya tafi kotun Duniya, ya nemi Najeriya ta yi kashin N200bn
Ministan harkar wuta, Saleh Mamman Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

KU KARANTA: Mambilla: Gwamnati ta ware N2.6b rak a matsayin gudumuwarta

A shekarar 2017 ne Ministan wutar lantarki na wancan lokaci, Babatunde Fashola, ya yi fatali da yarjejeniyar. ICIR ta ce hakan ya jefa gwamnatin kasar a matsala.

Ministan wutan ya ce gwamnatin tarayya ta na aiki ne kai tsaye da wani kamfani na kasar Sin da aka ba wannan kwangila watau Sinohydro Corporation Limited.

Hakan ya sa SPTCL ya shigar da kara, ya nemi a biya shi $2.354b saboda kin cika alkawari. Bayan Saleh Mamman ya shiga ofis, aka yi sulhun cewa za a biya $200m.

Dazu kun ji akwai yiwuwar Lauyoyin Najeriya su yi shari’a kan Twitter da Gwamnati a makon gobe bayan Kungiyar NBA ta tanadi Lauyoyi 13 da za su kai kara.

A gefe guda kuma Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami da takwaransa, Lai Mohammed ne za su jagoranci zama tsakanin Najeriya da kamfanin Twitter domin a sasanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel