Naira Ta Yi Tashin da Ba a Taba Gani ba a cikin Shekaru 2 a Kasuwa
- Naira ta kara samun karfi sosai a kasuwar gwamnati ta NFEM bayan ta kai ₦1,315 a kowace Dala ta Amurka
- Wannan ne karon farko da darajar kudin kasar ta kai wannan matsayi a cikin tsawon fiye da shekaru biyu
- Ba darajar Naira kadai ta tashi ba, an ga canji a asusun da Najeriya ta ke ajiye kudin kasashen waje a CBN
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Naira ta yi hobbasa a kasuwar canjin kudi da wani tashi da ta yi a ranar Alhamis, 3 ga watan Satumba 2026.
A farashin babban bankin Najeriya na CBN, an ji cewa an canza kudin Najeriyan a kan kowace Dalar Amurka a N1, 315.

Source: Getty Images
Alkaluman da aka samu daga kasuwar canjin Najeriya ta NFEM ta nuna Naira ta tashi a cewar rahoton da The Cable ta fitar.
Naira ta karu da 0.84% daga N1, 326 da aka saye Dalar Amurka a kasuwar a ranar Laraba wato 2 ga watan Satumba 2026.
Naira ta yi tashi mafi girma tun 2024
Rabon da a canza Dalar kasar Amurka kan N1, 300 tun a cikin watan Afrilun shekarar 2024.
Wannan tashi da kudin Najeriyan ya yi shi ne mafi girma da aka gani tun da babban bankin kasar ya fito da tsarin EFEMS.
Ta nan mutane suke samun kudin waje a yi dawainiyar tafiye-tafiye, ziyarar asibitoci da kudin makarantu a kasashen duniya.
Nawa Dala ta ke a hannun 'yan canji?
Haka labarin yake har hannun ‘yan kasuwa domin daga N1, 410 da aka canji Dala a ranar Alhamis, yau Juma’a ta koma N1, 400.
Tribune ta tabbatar da yadda darajar Naira ta karu da N11 a kan Dala a kafar EFEMS da CBN ya fito da shi a watan yunin 2023.
Da aka duba shafin Aboki FX mai bibiyar darajar kudin kasashen duniya, an ga cewa ana saida Dala guda a kan N1, 395 a jiya.
A yammacin na Alhamis, ‘yan kasuwa sun saye kudin Amurkan ne a kan N1, 405.
An samu wannan canji a kasuwar musayar kudin ne lokacin da ake farin ciki da cikar da asusun kudin kasar waje ya yi yanzu.
Asusun kudin kasar waje ya karu a 2026
Rahoton ya ce kudin waje ($54.08b) da aka tara a asusun kudin ketare ya yi tumbatsar da aka shafe shekaru 17 ba a ga irinsa ba.
Idan aka kamanta da $45.56bn da aka tara a farkon shekara, kudin asusun wajen ya karu da 18.69%, an samu karin $8.51bn.

Source: Getty Images
FWF: ‘A biya mu akalla N300, 000’
Rahoton nan ya ce ma’aikata sun nemi karin 320% a mafi karancin albashi domin abubuwa sun canza saboda manufofin gwamnati.
Ma'aikatan gwamnatin tarayya sun bukaci a kara albashi zuwa tsakanin ₦300,000 da ₦1.5m saboda tsadar rayuwa da ake fuskanta a yau.
Shugaban kungiyar FWF sun aika wa gwamnati takarda suna cewa kyau a sake yin karin albashi ba tare da an jira shekarar 2027 ba.
Asali: Legit.ng

