An Samu Magidancin da Ya Rasa Yara 6 da Sojoji Su Ka Kashe Masu Maulidi a Kaduna

An Samu Magidancin da Ya Rasa Yara 6 da Sojoji Su Ka Kashe Masu Maulidi a Kaduna

  • Wani Bawan Allah da ke zaune a kauyen Tudun Biri ya ce duka ‘ya ‘yansa shida sun rasu da aka jefo masu bam
  • Musa Umar ya bada labarin yadda ya rasu masoya a sakamakon kuskuren da dakarun sojoji su ke ikirarin sun yi
  • A lokacin da aka zanta da shi, Malam Musa Umar ya ce babu wani jami’in gwamnati da ya kai masu agaji

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Musa Umar mazaunin Tudun Biri ne a karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, inda sojoji su ka kashe masu maulidi.

A wata hira da gidan talabijin na Jakada ta yi da Malam Musa Umar, ya bada labarin yadda wannan masifar ta aukawa Tudun Biri.

Kara karanta wannan

Ba yau ne farau ba: Kwankwaso ya yi tir da Sojojin da su ka kashe mutane a Kaduna

Sojoji
Wani bam jirgin sojoji mara matuki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Magidanci ya sha da kyar a Tudun Biri

Kamar yadda bidiyon da aka wallafa ya nuna, magidancin ya samu rauni a sakamakon bama-baman da sojoji su ka harbo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Musa Umar ya ce lamarin ya rutsa da shi, a lokacin da su ke kokarin ceto wadanda aka fara harbawa bam, sai aka sake jefo wani.

Bayan harbo bam na biyun ya samu rauni wanda ya ce an yi masa magani a asibiti, sai dai har yanzu babu wani agaji da aka kawo.

A cewar magidancin bam din da sojoji su ka harbo ya yi jifa da shi, amma Allah SWT ya yi cewa ya na da rabon wasu kwanaki a gaba.

Bam 2 sojoji su ka jefa a Tudun Biri

Mutumin ya fadawa manema labarai da bam din farko ya sauko, shi da wasu mutane da yawa su ke kokarin ceto wadanda aka harba.

Kara karanta wannan

Ba kuskure ba ne: Ahmad Gumi ya dauki zafi a kan kisan masu taron Maulidi a Kaduna

Daga cikin wadanda ke tare da shi da aka jefo bam-baman da kimanin 11: 00 na dare akwai wani mai suna Jimrau da yanzu ya rasu.

"Na rungumi yaro na, na kai shi gefe ina neman babur da zai kai shi asibiti, sai aka sake jefowa.
Yaro na ko daya ba ya asibiti, duk sun rasu duka shidan, dukkansu sun rasu."

- Malam Musa Umar

A hirar da JKD TV ta yi da shi kamar yadda Abba Gwale ya wallafa bidiyon, shi kan shi Malam Musa Umar ya samu rauni a jiki da kai.

Ta’aziyyar Bukola Saraki ga mutanen Tudun Biri

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ya aiko ta’aziyya, ya ce:

“Kashe mutane ta hanyar harba musu bom da aka yi a lokacin da suke bikin Maulud a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna abin takaici ne.
Da ni da iyali na muna mika sakon ta'aziyyar mu ga al'umma da gwamnatin jihar Kaduna da iyalan wadanda wannan ibtila'i ya fadawa. Ina addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu sannan wadanda suka samu rauni kuma Allah ya ba su lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamnati Za Ta Biya Diyyar Mutane 85 da Sojoji Su Ka Kashe da Bam a Kaduna

Sai dai bayan wannan Mummunan ibtila'i, ya zama dole mu gujewa faruwar irin wannan a nan gaba. Sannan akwai bukatar a gudanar da bincike domin a gano yadda wannan abin ya faru sannan a kawo hanyoyin gujewa faruwar sa nan gaba.
Har ila yau, ya zama dole a sake nazari, wannan ya zama izina, bugu da kari a hada hannu waje guda wajen sake gina kishin kasa a zukatan mutane, adalci da kaunar juna domin tabbatar da kiyaye lafiyar duk wani dan kasa.”

- Bukola Saraki

Kwankwaso ya ji takaicin abin da ya faru

Ana da labari cewa Rabiu Kwankwaso ya ji takaicin samun labarin dinbin mutanen da aka kashe a kauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna.

Tsohon Ministan tsaron ya ce sakin bam da sunan ‘kuskure’ danyen aikin jami’an tsaro ne da aka saba yi a maimakon a kare al’umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel