Kansila ya yi wa matar yayansa mugun duka bayan zarginta da maita

Kansila ya yi wa matar yayansa mugun duka bayan zarginta da maita

- Ya zargi matar da maita kuma sun nada mata duka shi da kannen sa mata

- Yan uwansa sun shaidawa matar cewa babu abin da za ai bayan sun gama nada mata duka, tunda yayan su kansila ne.

- Rundunar yan sanda ta tabbatar da samun korafi kuma tace tana bincike

Wata mata mai yaya shida ta zargi Kansilan mazabar Etche, na karamar hukumar Etche a Jihar Rivers, Blackson Nwanyawu ta ji mata ciwuka kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Da take magana da manema labarai, matar wadda ta bayyana sunanta Love Nwanyawu, tace Kansilan wanda kanin mijinta ne, tare da abokansa biyu, sunyi mata dukan kawo wuka.

Love, wadda fuskarta take a kumbure da kuma kujewa a wasu sassan jikin ta, tace abin ya faru lokacin ta kai ziyara garinsu mijinta a yankin Omualu, Etche.

Naji muryarsa shi da yan uwansu mata guda biyu.

Kansila a jihar Rivers ya yi wa matar yayansa mugun duka
Kansila a jihar Rivers ya yi wa matar yayansa mugun duka. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wasu mazauna Kaduna sun soki harajin cigaba na N1,000 da gwamnati ta sakawa duk baligai

"Nayi mamaki, kawai sai naga su ukun sun taho kaina, suka ce ina takura musu kuma wai ni mayya ce. Suka ce wai in dai nazo ba'a zaman lafiya a gidan, nace musu ta yaya?

"Suka min duka. Bayan sun dake sun rufe ni a daki, sai daya daga cikin su ya samo kujera ya buga min a kaina har sau biyu. Da Kansilan yaga jini sai ya gudu. Suma sai suka gudu. Da jinin a jikina na nemi taimako sai suka ce ba abin da zai faru ai dan uwansu kansila ne.

"Ina so mutane su taimaka wajen kwato min yanci. Miji na ne ya dauki nauyin karatunsa daga sakandire har jami'a. Ni na biya kudin makarantarsa na karshe kuma ya taba cewa idan ya gama karatu, yara na baza su sha wahala ba.

"Na tambaye shi wannan ne alkawarin da kayi min? Kalli yadda ka maida ni. So yake ya kashe ni," a cewar Love.

KU KARANTA: Cibiyar Lafiya ta ce ana fuskantar karancin kororon roba a wani gari a Bauchi

Matar tace mijinta ya dade yana jiyya kuma ya dimauta sosai da ya samu labari.

Sai dai da aka ji ta bakin Kansilan, cewa yayi matar yayan nasa zagin shi tayi, ya bayyana haka a wata waya da suka yi da yar matar yayan nashi.

"Maman kullum sai ta zage ni. Babanku ya kirani kuma na fada masa banyi nadamar abin da ya faru ba, nayi iya juriyata," a cewar shi.

Ya ce zai amsa gayyatar da yan sanda ke masa.

"Wannan ba wani abu bane amma in kana irin wannan mataki dole haka ya faru, zan je ofishin yan sandan gobe don kare kaina," ya sake nanatawa.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Nnamdi Omani, ya tabbatar da sun karbi korafin kuma suna binkice.

A wani labarin, Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, ya gaya wa shugabancin jam'iyyar PDP a Abuja ranar Talata cewa zai bar jam'iyyar.

Ya ce zai koma jam'iyya mai mulki ta APC yana mai ikirarin cewa APCn zata bawa dan yankin sa na kudu maso gabas takara a zaben 2023.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel