Yadda maita ke janyo lalacewar yara a Najeriya - Rahoton Aljazeera

Yadda maita ke janyo lalacewar yara a Najeriya - Rahoton Aljazeera

- Ana yi wa yara sharrin cewa wai su mayta a kudancin Najeriya

- Ana azabtar dasu da ruwan zafi da wuta, kuma iyayensu ke kaisu

- An sami masu cetonsu amma turawa ne daga wata kasar

Yadda maita ke janyo lalacear yara a Najeriya - Rahoton Aljazeera
Yadda maita ke janyo lalacear yara a Najeriya - Rahoton Aljazeera
Asali: UGC

Addinin da ake bi a yankin kudancin Najeriya yana karfafa camfin cewa wai ana haifar yara da maita, matsala dake jefa su cikin halin ha'ula'i, ana azabtar dasu, kuma matsalar shine gwamnatin tayi gum da bakin ta shekara da shekaru.

Yara a yankin Naija Delta da aka danganta da maita na shiga cikin mugun hali. Akan duke su, hana su abinci, wasu ma har kona su ake da wuta. Yara sama da 15,000 na yankin aka danganta da maita a cikin karnin da ya gabata

Yaran yankin Naija Delta da aka danganta da maita na fuskantar kalubale kala kala. Kama daga duka, hana su abinci, kai har ma da kona su da wuta.

Sama da yara 15,000 a yankin akan danganta da maita a karnin da ya gabata.

Malaman addinai sun saba danganta yara da maita a Najeriya. Wasu kuma Malaman kan kokarin raba yaran da maitar.

DUBA WANNAN: Buhari ya soki Atiku kan re-structuring

Kamfanin fina finan Nollywood ma ya taka rawar gani gurin cusa ma mutane yarda da maita.

A shekara ta 2008, Najeriya ta fara yunkurin yanke shekaru 10 a gidan yari ga duk wanda aka danganta da maita, wanda har yanzu ba' zartarwa kowa ba.

Iyayen yaran dai ke kai 'ya'yan da kansu, wurin masu wai aikin warkar dasu, da azaba da magunguna da addu'o'in coci.

Aljazeera ce dai ta bi kadin lamarin, inda ta saki rahoton bayan binciken karkashin kasa da ma na jin ta-bakin jama'a.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel