Za’a rataye wani matashi daya daddatsa matar babansa akan zargin maita

Za’a rataye wani matashi daya daddatsa matar babansa akan zargin maita

Wata babbar kotun jahar Filato dake zamanta a garin Jos ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya akan wani matashi mai suna Binfa Lamde, mai shekaru 24 wanda take zargi da aikata laifin kisan kai bayan ya kashe kishiyar babarsa.

Legit.com ta ruwaito Alkalin kotun, mai sharia A.I Ashoms ya bayyana cewa matashin ya cancanci hukuncin kisa ne bayan ya kamashi dumu dumu da laifin halaka matar babansa mai suna Kum Zwade.

KU KARANTA; Gwamnati zata kafa hukumar da zata kula da Kaduna, Kano, Katsina Jigawa, Sokoto, Kebbi da Zamfara

Da yake yanke hukuncin, Mai sharia Ashoms ya bayyana cewa “Biyo bayan binciken da kotu ta gudanar, mun gano Lamde ya nuna rashin Imani tsantsa akan matar babansa Kum Zwade, inda ya kasheta yayin da take cikin barci.

“Don haka wajibi ne na yanke masa hukuncin kisa saboda doka tace duk wanda aka kama shi da laifin kashe wani, shima hukuncinsa kisa ya dace akansa ta hanyar rataya, don haka hukuncin da wannan kotu ta yanke maka, Binfa Lamde shine za’a ratayeka har sai ka mutu. Allah yayi maka rahama” Inji Ashom.

A shekarar 2014 aka fara gurfanar da Lamde a gaban kotu, inda ake tuhumarsa da laifin kisan kai, wanda ya saba ma sashi na 221 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Filato, inda ake tuhumarsa da kashe matar babansa a ranar 10 ga watan Afrilun 2014.

Shima a jawabin ma Yansanda, Lamde ya bayyana cewa shi ne ya kashe matar a kauyensu dake Ngwak, cikin karamar hukumar Langtang ta Arewa, saboda a cewarsa mayyace ta kama kanwarsa da suke uba daya, Chakwai Zuwade, diyar matar kenan.

Hakanan Lamde ya kara da cewa baya ga kama kurwar diyarta, kishiyar babar tasu ta kama dansa, kuma ta tabbatar musu da ita ta kama Chakwai, amma duk magiyan da suka yin a ta sakesu ta ki, don haka ya bita da adda cikin daki yayin da take barci ya daddatsata gunduwa gunduwa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng