Shugaban Kwastam Ya Bayyana a Gaban Majalisa, Ya Faɗi Gaskiya Kan Siyar da Kayan Abinci Ga Talakawa

Shugaban Kwastam Ya Bayyana a Gaban Majalisa, Ya Faɗi Gaskiya Kan Siyar da Kayan Abinci Ga Talakawa

  • Hukumar kwastam ta ƙasa ta bayyana cewa ta fara siyar da kayan abincin da ta ƙwace ga talakawan Najeriya domin tsamo su daga kangin yunwa
  • Shugaban hukumar kwastam, Adewale Adeniyi ne ya sanar da haka yayin da ya bayyana a zauren majalisar wakilan tarayya
  • Ya ce shugaban ƙasa ya bai wa NCS umarnin sayar da abincin a farashi mai sauƙi yayin da abincin ƙasar waje kuma za a shigar da su kasuwanni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar Kwastam ta Najeriya ta fara sayar da kayan abinci da aka kama ga mabukata a Najeriya domin magance yunwar da ake fama da ita a fadin kasa.

Shugaban kwastam na ƙasa, Adewale Adeniyi, ne ya sanar da haka yayin da ya bayyana a gaban majalisar wakilan tarayya ranar Talata, 5 ga watan Maris, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta bayyana ainihin abin da ya jawo karancin abinci da tsadar rayuwa

Kwastam ta fara siyar da kayan abinci ga yan Najeriya.
Shugaban Kwastam Ya Bayyana a Gaban Majalisa, Ya Fadi Taimakon da Zasu Ba Yan Najeriya Hoto: Nigerian Customs
Asali: Twitter

Mista Adeniyi ya halarci mahawarar da majalisar ta shirya kan wadatar abinci a ƙasa tare da ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari, The Nation ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin a sayar da kayan abincin da ake nomawa a Najeriya wanda NCS ta kama a kan iyakoki kai tsaye ga ‘yan Najeriya masu rauni.

Wane mataki ake ɗauka don magance yunwa?

Ya ce wannan matakin zai taimaka wajen magance ƙalubalen yunwa da ƴan Najeriya ke fama da ita a halin yanzu, kamar yadda jaridar Punch ta tattaro.

A jawabinsa, kwanturola janar na kwastam ya ce:

"Shugaban ƙasa ya bamu umarnin mu sayar da kayayyakin abincin da aka noma a gida Najeriya amma kuma muka kwace su saboda wasu dalilai.
"Wannan yana daya daga cikin hanyoyin magance yunwa da karancin abinci da muke fuskanta. Mun fara sayarwa a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya zo yayin da Gwamnatin Tinubu za ta fara rabon kayan abinci kyauta a jihohin Najeriya

"Har ila yau, shugaban kasa ya ba mu umarnin sayar da kayan abincin da NCS ta kama daga kasashen waje ga kasuwannin cikin gida domin sake sayar wa ‘yan Najeriya."

Wannan dai na zuwa ne awanni bayan ministan noma, Abubakar Kyari ya tabbatar da cewa za a fara raba hatsi tan 42,000 ga ƴan Najeriya a makon nan.

Malami ta tallafawa mabiya da kayan abinci

A wani rahoton kuma kun ji cewa wani Fasto na cocin Dunamis International Church a Uyo ya rabawa mabiyansa tallafin kayan abinci domin rage masu raɗaɗi.

Malamin addinin ya rabawa mabiyansa masu zuwa ibada a cocin kayan abinci da suka haɗa da shinkafa, doya da sauran kayan amfani na yau da kullum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel