Ba Maganar Gyaran Lantarki, Dan Takarar Shugaban Kasa Zai Saka wa Kowa ‘Solar’

Ba Maganar Gyaran Lantarki, Dan Takarar Shugaban Kasa Zai Saka wa Kowa ‘Solar’

  • Wanda ke takarar shugaban kasa a SDP, Adewole Adebayo, ya yi alkawarin samar da wutar hasken rana ga kowane gida cikin watanni 11
  • Adebayo ya ce gwamnatinsa za ta gina masana’antun kera bangarorin hasken rana, tare da horar da ’yan Najeriya aikin
  • Ɗan takarar SDP ya ce tarukan hasken rana za su samar da wutar bukatun gidaje, ayyukan yi da kuma samar da megawatt 32,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na Social Democratic Party (SDP), Adewole Adebayo, ya bayyana abin da zai yi bayan an zabe shi a 2027.

Adebayo ya yi alkawarin samar da hasken rana ga kowane rufin gida cikin watanni 11 idan aka zaɓe shi.

Alkawarin da dan takarar shugaban kasa ya yi
Dan takarar shugaban kasa, Adewole Adebayo. Hoto: @Pres_Adebayo, @Tinsley_Ks.
Source: Twitter

Adebayo ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin wata hira da gidan talabijin na Arise a shirin Prime Time, inda ya bayyana shirinsa kan wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Dan takara ya yi alkawarin samar da lantarki a kowane gida cikin watanni 11 a Najeriya

Alkawarin da Adebayo ya yi

Ya ce gwamnatinsa za ta gina masana’antun kera bangarorin hasken rana a faɗin ƙasar, tare da horar da ’yan Najeriya girkawa da kuma kula da tsarin wutar.

A cewarsa, tarukan samar da hasken rana da aka tsara za su samar da wutar da gidaje ke buƙata, da ayyukan yi, tare da samar da megawatt 32,000.

Ya ce:

“Na yi alkawarin cewa za a sanya hasken rana mai ƙarfin kilowatt 11 zuwa 15 a kan kowane rufin gida cikin watanni 11.
“Za ku haɗa dukkan waɗannan, ku samar da ayyukan yi, sannan ku samar da megawatt 32,000 daga waɗannan taruka. Daga nan sai ku bar shi.
“Na gaya musu cewa haka za mu tafiyar da layin wutar lantarki na ƙasa. Layin wutar lantarki na ƙasa zai kasance madadin gaggawa. Idan wani taro ya samu matsala, za ku samu wuta daga can."
Adebayo ya yi alkawarin samar da 'solar'
Adewole Adebayo da ke takarar shugaban kasa a inuwar SDP Hoto: @Pres_Adebayo.
Source: Twitter

Yadda Adebayo zai inganta rayuwar matasa

Kara karanta wannan

'Neman fitina yake yi': Gwamnatin Benue ta yi martani mai zafi bayan jifan Peter Obi

Ɗan takarar SDP ya ce za a iya kafa masana’antun ne ta hanyar haɗin gwiwa da ƙasashe irin su China, Turkiyya da Indiya, yayin da za a horar da ’yan Najeriya su gudanar da ayyukansu.

Ya ce a baya ya taɓa ba gwamnati shawara kan batutuwan wutar lantarki, sannan ya gwada fasahar hasken rana a garinsu, inda ya ce ya horar da kusan mutane 2,000.

Adebayo ya ce:

“Na yi wani gwaji a garina. Ina da kusan mutane 2,000 da na horar kan hasken rana, saboda ni da kaina nake kera bangarorin hasken rana. Ina kuma kera batirin lithium."

Adebayo ya kuma ba da shawarar gwamnati ta zuba jari a muhimman fannoni kamar su harkar jiragen sama da masana’antu, maimakon barin su gaba ɗaya hannun kamfanoni masu zaman kansu, cewar Punch.

Adebayo ya tsoratar da Tinubu kan zaben 2027

Mun ba ku labarin cewa dan takarar shugaban ƙasa na SDP, Adewole Adebayo, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba wanda ba za a iya kayarwa ba ne a zaɓen 2027.

Adebayo ya ce APC za ta zo ta ƙarshe, yana mai cewa sakamakon zaɓen zai dogara ne kan ƙuri’un da ’yan Najeriya za su jefa.

Ɗan takarar ya ce Najeriya na da damar noma da za ta iya ba Afirka abinci, amma rashin isasshen jari ya hana bunƙasar fannin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.