Da Matsala: Farashin Fetur Ya Kara Tsada duk da Saukin da Aka Samu a Wuraren Sari a Najeriya
- Ko
- Farashin fetur a rumbunan ajiya ya sauka a wasu sassan Najeriya amma gidajen mai suna ci gaba da sayar da shi da tsada
- A jihar Legas, farashin litar fetur a wurin safi ya kai tsakanin N1,266 zuwa N1,280 ranar Talata da ta gabata
- Masu harkar man fetur sun ce kudin sufuri da sauran kashe-kashe na iya kara tazarar farashin sari da kuma na gidajen mai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Rahotanni sun nuna cewa farashin fetur na ci gaba da tashi gidajen mai a fadin Najeriya duk da raguwar farashin da ake sayar da shi a wuraren ajiya watau farashin sari.
Sababbin alkaluman farashin man fetur da aka fitar da tsakar ranar Talata, 8 ga watan Satumba, 2026, sun nuna cewa ana sayar da lita tsakanin N1,266 zuwa N1,280 a wasu manyan wuraren dillancin mai da ke Legas.

Source: Getty Images
Vanguard ta rahoto cewa wannan lamari ya sake tayar da tambayoyi kan dalilin da ya sa ake samun tazara mai yawa tsakanin farashin sari da kuma farashin da yan Najeriya ke biy a gidajen mai
Farashin fetur a wuraren sari a Legas
Matatar Dangote da Pinnacle sun sayar da litar fetur kan N1,266, yayin da MRS ke sayarwa kan N1,267.
Aiteo, Integrated da Sahara kuwa sun sayar da litar man kan N1,270, yayin da Ascon da NIPCO suka sanya farashin N1,280.
Wannan ya nuna cewa mafi karancin farashin fetur da aka samu a wurren sari a Legas ya yi kasa da N44 idan aka kwatanta da N1,310, wanda shi ne mafi karancin farashin da aka samu a wasu gidajen mai.
Sai dai gidajen mai da dama a Legas da Abuja har yanzu suna sayar da litar fetur kan N1,325 ko sama da haka.
Masu bada sari sun rage farashi

Kara karanta wannan
Peter Obi ya bada mamaki, ya halarci ƙaddamar kamfe na wani ɗan takarar shugaban kasa a 2027
Alkaluman sun kuma nuna cewa wasu manyan wuraren daukar sarin fetur sun rage farashin fetur dinsu, Integrated da Sahara da ke Legas sun rage da N9 kan kowace lita zuwa N1,270.
Lister kuma ya rage farashinsa da N3 zuwa N1,277 kan kowace lita. A Warri, Bulk Strategic, Liquid Bulk da Masters sun rage farashi da N10 kan kowace lita.
Matrix ya rage nasa farashin da N5, yayin da Rain Oil ya yi mafi girman ragi bayan ya sauke farashin da N20 zuwa N1,280 kan kowace lita.
Me ke jawo tazarar farashin?
Babban bambanci tsakanin farashin sayen fetur daga wuraren sari da farashin da ake sayarwa ga masu amfani ya ja hankalin masu ruwa da tsaki kan karin kudaden da ake kashewa bayan an fitar da man daga depuna.
Masu harkar kasuwar man fetur sun ce kudin sufuri da rarrabawa na daga cikin muhimman abubuwan da ke tasiri kan farashin da yan Najeriya ke biya a gidan mai.

Source: Getty Images
Wani mai gudanar da harkokin sayar da mai ya ce bambancin farashin na iya kasancewa sakamakon hanyoyin samun mai da tsarin kasuwancin gidajen mai daban-daban.
Ya ce:
"Ba kowane gidan mai ne ke sayen fetur kan farashi iri daya ba. Wurin da gidan mai yake, kudin sufuri da sauran kashe-kashe duk suna tasiri kan farashin da ake sayarwa."
Matatar Dangote ta kara farashin mai
Kun ji cewa matatar Dangote ta kara farashin fetur da N65, inda farashin ya tashi daga N1,200 zuwa N1,265 kan kowace lita.
Karin na baya-bayan nan shi ne na uku cikin kwanaki takwas, inda jimillar karin farashin fetur ya kai N100, wato kashi 8.6 cikin 100
Asali: Legit.ng

