Ba zan iya bar wa mijina diyana ba, wata mata shaidawa kotu

Ba zan iya bar wa mijina diyana ba, wata mata shaidawa kotu

Wata mata mai suna Jamila Muhammad a ranar Talata 24 ga watan Satumba, 2019 ta roki Kotun Shari’a dake Rigasa a garin Kaduna da ta bata alhakin rike diyanta uku.

Jamila ta fadi a cikin korafinta ga kotun cewa akwai yiwuwar yaran za su iya shiga matsanancin hali idan ta bar su a hannun mahaifinsu wato Sani Umar.

KU KARANTA:Majalisar dinkin duniya ta nada Dangote da Adesina cikin wani kwamitin mutum 27 (Jerin sunaye)

Har ila yau, Jamila ta kara da cewa maigidan nata ya yi mata furucin saki har sau biyu kuma ya raba da diyanta ta hanyar amfani da karfi.

“Ya kwashe min yarana yayi gaba da su, a ciki hadda jaririn da nake shayarwa. Sai bayan kwana uku da kotu ta tursasa shi sannan ya maido min da dana.

“Ina so in roki wannan kotu mai adalci da ta bani hurumin rike diyana saboda karamar diyata ta bani labarin cewa ‘ya uwan uban sun fara muzguna ma ta.” Inji Jamila.

Da yake martani game da kararsa da aka shigar a kotun Shari’a ta Rigasa, Umar ya karyata abinda matarsa ta fadi.

Bugu da kari, iyalan bangarorin biyu sun halarci wannan kotu domin samar wa ma’auratan da masalaha guda daya.

Alkalin kotun, Mallam Dahiru Bamalli bayan ya saurari jawabai daga bangarorin matar da mijinta ya ce shari’a ta haramta a raba uwa mai shayarwa da jaririn da take shayarwa.

Sannan kuma a karshe ya nemi mijin da ya kawo yaran nasa a gaban kotu ranar Laraba 25 ga watan Satumba, 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel