Samia Suluhu: An Shiga Jimami da Shugabar Kasar Tanzania Ta Yi Babban Rashi a Rayuwa
- Hafidh Ameir Hassan, mijin shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan, ya rasu da safiyar Litinin 7 ga Satumba 2026 yayin da yake jinya
- Mataimakin Shugaban Tanzania Deogratius Ndejembi ya tabbatar da rasuwar, yana mai cewa Hafidh ya rasu da misalin ƙarfe 8:00 na safe a Zanzibar
- Shugaban Rwanda Paul Kagame ya jajanta wa Samia da al’ummar Tanzania, yana mai bayyana shugabar a matsayin “’yar uwarsa” tare da girmama rayuwar marigayin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Tanzania - Tanzania na jimamin rasuwar Hafidh Ameir Hassan, mijin Shugabar ƙasar Samia Suluhu Hassan, wanda ya rasu da safiyar Litinin, 7 ga Satumba 2026.
Rahotanni sun bayyana cewa Hafidh ya rasu ne yayin da yake karɓar magani a wani asibiti da ke Zanzibar.

Source: Twitter
Kamfanin dillancin labarai na Capital FM Kenya ya ruwaito cewa Mataimakin Shugaban Tanzania, Deogratius Ndejembi, ne ya sanar da rasuwar a hukumance.
Hafidh ya rasu yana karɓar magani
Ndejembi ya ce Hafidh ya rasu da misalin ƙarfe 8:00 na safe a Mlimani Mzena Memorial Hospital da ke Zanzibar.
Ya bayyana cewa marigayin yana karɓar magani ne sakamakon wata matsalar zuciya kafin rasuwarsa.
BBC ma ta bayar da rahoton rasuwar Hafidh, lamarin da ya jefa Tanzania cikin zaman makoki.
Da yake sanar da rasuwar, Ndejembi ya ce:
“Cike da matuƙar baƙin ciki nake sanar da ku rasuwar Mai Girma Hafidh Ameir Hassan, mijin Shugabar Jamhuriyar Tarayyar Tanzania, Mai Girma Dr Samia Suluhu Hassan.”
Mataimakin shugaban ƙasar ya miƙa ta’aziyyarsa ga Shugaba Samia, iyalanta da sauran mutanen da ke kusa da ita a wannan lokaci na baƙin ciki.
“Ina miƙa ta’aziyyata mafi zurfi ga Mai Girma Shugabar ƙasa, iyalanta, ’yan uwa, abokai da kuma dukkan ’yan Tanzania a wannan lokacin na jimami.”
Za a binne Hafidh a Zanzibar
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce tuni aka fara shirye-shiryen jana’izar marigayin.

Kara karanta wannan
"Musulunci ya yi rashi," Sarkin Musulmi ya shiga alhini bisa rasuwar Sarki mai martaba a Najeriya
A cewarsa, za a binne Hafidh Ameir Hassan a Kizimkazi, Zanzibar, inda za a gudanar da jana’izar bisa tsarin da hukumomin ƙasar za su sanar.
Rasuwar Hafidh ta jawo ta’aziyya daga shugabannin ƙasashe da sauran manyan mutane yayin da Tanzania ke jimamin rashin.
Kagame ya jajanta wa Shugaba Samia
A wani ɓangare kuma, Shugaban Rwanda Paul Kagame ya miƙa saƙon ta’aziyya ga Shugabar Tanzania bayan rasuwar mijinta.
Kagame ya bayyana Samia a matsayin “’yar uwarsa”, yayin da yake jajanta mata, iyalanta da al’ummar Tanzania kan wannan babban rashi.
A cikin saƙon ta’aziyyarsa wanda ya sanya a shafin X, Kagame ya ce gwamnatin Rwanda da al’ummar ƙasar suna tare da Shugaba Samia da ’yan Tanzania a lokacin da suke jimamin rasuwar Hafidh da kuma karrama rayuwarsa da abubuwan da ya bari.

Source: Twitter
Jarumar fim Zainab Diamond ta rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Jarumar shirin fim din Hausa na Labarina, Zainab Diamond, wadda aka fi sani da Maman Bintalo, ta rasu bayan fama da doguwar jinya.
Rasuwar jarumar ta faru ne bayan Sallar Asuba, inda labarin ya jefa ‘yan uwa, abokan aiki da masoyanta cikin jimami.
Asali: Legit.ng
