Waiwaye: Can baya, hoton lokacin da Abba Kyari ke da'awar yaki da shan kwayoyi

Waiwaye: Can baya, hoton lokacin da Abba Kyari ke da'awar yaki da shan kwayoyi

  • An hangi DCP Abba Kyari a cikin wani hoto da ya fito yana nuna kin jinin shan kwaya, inda yake yaki da shan miyagun kwayoyi
  • An yada hoton a yanar gizo jim kadan bayan gano yana harkallar kwaya, bayan da NDLEA ta kama shi hannu dumu-dumu
  • Dan sandan da aka dakatar a 2021 lamarinsa ya fita fili a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu bayan hukumar NDLEA ta bayyana cewa tana neman sa ruwa a jallo

A kwanakin baya ne wani hoton dakataccen shugaban tawagar leken asiri ta IRT, DCP Abba Kyari ya fita, inda ya shiga sahun yaki da shan miyagun kwayoyi, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne sa'o'i bayan tsare babban jami'in 'yan sandan bisa zarginsa da alaka da wata tawagar masu safarar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa.

Kara karanta wannan

Abba Kyari: Ba zamu yi rufa-rufa ba, duk wanda ke da hannu zai gurfana: NDLEA ta yiwa IGP martani

Lokacin da Kyari ke yakar shan kwayoyi
Waiwaye: Can baya, lokacin da Abba Kyari ke da'awar yakida shan kwaya | Hoto: @General_Somto
Asali: Twitter

Idan za a iya tunawa, wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda, Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ta bayyana cewa ‘yan sandan Najeriya sun kama Kyari tare da wasu jami’ai hudu a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta bayyana cewa tana neman babban dan sandan da aka dakatar bisa zarginsa da hada baki da masu safarar miyagun kwayoyi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Femi Babafemi, mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, ya ce hukumar ta yi imanin cewa "DCP Kyari mamba ne na wata tawagar masu safarar miyagun kwayoyi da ke gudanar da haramtacciyar harkallarsu a kasashen Brazil da Habasha da Najeriya".

Kwamitin bincike ya bukaci a rage wa Abba Kyari matsayi zuwa ACP

Bayan watsi tare da komawa da binciken a kwamiti na musamman da ke bincikar dakataccen kwamandan IRT, DCP Abba Kyari kan $1.1 miliyan na damfarar da Hushpuppi, da kuma umarnin hukumar kula da ayyukan 'yan sanda na yin sabon bincike, DIG Joseph Egbuniike ya bukaci a rage wa Abba Kyari matsayi.

Kara karanta wannan

Daga Sarki ya zama Bawa: Rayuwar Abba Kyari a baya kadan da kuma yanzu

Wannan na zuwa ne bayan kwamitin ya tabbatar da cewa Abba Kyari ya hada kai da masu damfara, hakan kuwa ya yi karantsaye ga dokokin ayyukan 'yan sandan Najeriya, Vanguard ta ruwaito.

Baya ga haka, kwamitin binciken ya kama dan sandan da take dokokin soshiyal midiya ta hukumar 'yan sandan Najeriya ta yadda ya yi martani ga tuhumar FBI a shafinsa na Facebook ba tare da ya bi matakan da suka dace ba, wanda daga bisani ya goge martanin.

Abba Kyari: IGP ya bada umarnin rufe dukkan sassan IRT da STS na 'yan sandan Najeriya

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya bada umarnin rufe dukkan sassan rundunar binciken sirri na Intelligence Response Team da Special Tactical Squad a fadin kasar nan.

Wannan na zuwa ne bayan damke dakataccen mataimakin kwamishinan 'yan sanda kuma shugaban rundunar IRT na 'yan sandan Najeriya, Abba Kyari da wasu sakamakon zarginsu da ake da harkar safarar miyagun kwayoyi, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: NDLEA Ta Fara Yi Wa Abba Kyari Zafafan Tambayoyi a Ofishinta

Dukkan jami'an 'yan sanda da ke sassa a fadin kasar nan an bukaci da su kai kansu hedkwatar hukumar 'yan sanda da ke Abuja domin karin bayani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel