Jami’an ’Yan Sanda A Abuja Sun Kama Mutane 14 Kan Zargin Yada Karya Na Satar Mazakuta

Jami’an ’Yan Sanda A Abuja Sun Kama Mutane 14 Kan Zargin Yada Karya Na Satar Mazakuta

  • Rundunar ‘yan sanda a birnin Tarayya Abuja ta sanar da kama mutane 14 kan zargin yada karya da ke ta da hankula
  • Kwamishinan ‘yan sanda a birnin, Haruna Garba shi ya bayyana haka a jiya Talata 3 ga watan Oktoba a birnin Abuja
  • Ya ce sun gurfanar da mutanen a gaban kotun bayan likitoci sun tabbatar mazakutar tasu na nan ba abin da ya same su

FCT, Abuja – Jami’an ‘yan sanda a birnin Tarayya Abuja sun gurfanar da wasu mutane 14 kan yada karyar sace musu mazakuta.

Kwamishinan ‘yan sanda a birnin, Haruna Garba shi ya bayyana haka a jiya Talata 3 ga watan Oktoba a Abuja.

'Yan sanda sun cafke mutane 14 kan zargin yada karya na satar mazakuta
Jami’an ’Yan Sanda a Abuja Sun Cafke Mutane 14 Kan Yada Karerayi. Hoto: Nigeria Police.
Asali: Facebook

Meye 'yan sanda su ka ce kan satar mazakuta?

Ya ce jami’ansu sun samu rahotanni fiye da 10 na satar mazakuta a birnin wanda ya ke jawo daukar doka a hannu da mutane ke yi, Leadership ta tattaro.

Kara karanta wannan

Muhammadu Buhari: Babban Sakona Ga Mutanen Najeriya a Ranar Murnar 'Yancin Kai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Garba ya ce jami’ansu sun ceto rayuka da dama a kan karerayin satar mazakuta da mutane ke yi don tabbatar da doka da oda a birnin.

Ya ce an kama mutane 14 da ke yada cewa an sace musu mazakuta inda aka kaisu asibiti aka kuma tabbatar da mazakutar su na nan ba abin da ya same su.

Daga bisani an gurfanar da su a gaban kotu kan zargin yada karya da kuma ta da hankulan jama’a.

Wane gargadi 'yan sanda su ka yi kan satar mazakuta?

Kwamishinan ya gargadi mutane da su guji yada karerayin cewa an sace musu mazakuta ba tare da sun tabbatar ba inda ya ce hakan ka iya jawo rasa rayuka na mutane, cewar Vanguard.

Ya ce:

“Ina so na yi amfani da wannan dama wurin rokon mutane da su gargadi ‘ya’yansu wurin yada karya irin wannan.

Kara karanta wannan

Za a Fasa Shiga Yajin-Aiki a Najeriya, Gwamnati Ta Shawo Kan Kungiyoyin Ma’aikata

“Dadi da kari, bai kamata mutane su na daukar doka da hannunsu ba wanda ke jawo rasa rayuka da dama a dalilin haka.”

Matasa sun cinna wa coci wuta kan zargin satar mazakuta

A wani labarin, wasu fusatattun matsa sun cinnawa coci wuta saboda zargin satar mazakuta da ake zargin mai cocin a Taraba.

Matasan sun yi zanga-zanga don nuna damuwarsu bayan satar mazakutan mutane shida a kankanin lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel