Tinubu Zai Rabawa 'Yan Najeriya N25,000 Duk Wata, An Sake Cin Bashi
- Gwamnatin Tarayya ta sake ciro tsabar kudi dala miliyan 208.29 daga basussukan da Bankin Duniya ya amince mata
- Wadannan kudade dai suna cikin adadin bashin dala miliyan 800 ne na fadada shirin tallafin jin dadin jama'a a Nijeriya
- Ya zuwa yanzu Gwamnatin Tarayya ta karbi kusan 93.1% na jumillar tsarin bashin gaba daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Gwamnatin Tarayya ta samu damar ciro karin kudi dala miliyan 208.29 daga cikin bashin dala miliyan 800 da Bankin Duniya ya amince mata a karkashin shirin fadada tsarin tallafin jin dadin jama'a.
Bayanai daga kudin da aka ciro sun nuna cewa kudaden sun karkata ne a cikin kashi uku a rabin farko na shekarar 2026.
An saki dala miliyan 8.29 a ranar 8 ga Afrilu, da dala miliyan 150 a ranar 29 ga Afrilu, sannan aka kara sakin dala miliyan 50 a ranar 22 ga Yuni.
Irin wannan ciro kudaden ya sa jimillar kudaden da Najeriya ta sa hannu a kansu a wannan tsarin ya kai kusan dala miliyan 744.61. A halin yanzu, dala miliyan 55.39 kawai ke ajiye da ba a ciro ba tukuna.

Source: Facebook
Tarihin Bashin da Shirin Tallafin Kudi
Bankin Duniya ya amince da wannan rance na dala miliyan 800 ne a watan Disamba na shekarar 2021 ta hanyar Hukumar Inganta Ci Gaba ta Kasa da Kasa (IDA).
Babban makasudin karbo kudin shi ne fadada tallafin jin dadin jama'a ga gidaje matalauta da gina tsarin kariya a kasar.
Bayan janye tallafin man fetur a watan Mayun 2023, shirin ya samu muhimmanci sosai sakamakon matsin lamba a tattalin arzikin iyali.
Da farko dai, gwamnati ta tsara biyan N5,000 ne a kowane wata kafin daga bisani ta gyara adadin zuwa N25,000 na tsawon watanni uku ga miliyoyin 'yan Nijeriya.
Kiyaye Zamba da Bin Dokokin Tattalin Arziki
Domin dakile maganganun almundahana da zargin tafka magudi da aka gani a Ma'aikatar Jin Dadin Jama'a, gwamnati ta tsaurara hanyoyin tantance masu cin moriyar shirin.
A halin yanzu, ana amfani da Lambar Tabbatar da Asusun Banki (BVN) da Lambar Gane dan Kasa (NIN) kafin ba da tallafin.
Bayanan da aka sun nuna cewa sama da mutane miliyan 42 ne suka riga suka karbi tallafin kudin ta hanyar zamani da aka kirkiro a karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
A halin da ake ciki kuma, gwamnatocin na kokarin samun wani sabon rancen dala biliyan 1.25 daga Bankin Duniya domin bunkasa zuba jari da samar da ayyukan yi kafin zaben 2027.
Shirin Tinubu na gyara tattalin arziki
A wani labarin, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu fashi a kan sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ke aiwatarwa a ƙasar nan.
Shugaban ƙasan wanda aka zaba a 2023 ya jaddada cewa Najeriya ta shiga yanayin da dole sai an yi gyara, saboda haka ba za yi wasa da aikin da aka ɗauko ba.
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Tinubu ya faɗi haka ne a ranar Talata, 4 ga watan Fabarairu 2026 a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Asali: Legit.ng

