Kamfanonin Wuta Sun Karbi N1.2tr a Hannun 'Yan Najeriya Cikin Watanni 6

Kamfanonin Wuta Sun Karbi N1.2tr a Hannun 'Yan Najeriya Cikin Watanni 6

  • Kamfanonin raba wutar lantarki 11 a Najeriya sun tara judi kimanin N1.502tr tsakanin watan Janairu da Yuni na 2026
  • Ikeja Electric da Eko DisCo ne suka fi samun kudin shiga, yayin da Yola DisCo ta samu mafi karantan kudi a tsakanin kamfanonin
  • Kaduna DisCo ta gaza karbar fiye da kashi 48% na kudin da ta fitar, lamarin da ya sanya ta zama ta karshe a fannin aiki a 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT Abuja - Kamfanonin raba wutar lantarki 11 a Najeriya (DisCos) sun samu nasarar tara tsabar kudi N1.2tr daga hannun abokan cinikinsu tsakanin watan Janairu da Yuni na shekarar 2026.

Duk da wannan nasara, kusan N301bn na kudin wutar lantarki ne bai fito daga hannun jama'a ba a tsawon wannan lokaci, kamar yadda rahotannin kasuwanci na Hukumar Kula da Harkokin Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) suka bayyana.

Nassoshin bayanai daga NERC sun nuna cewa kamfanonin raba wutar sun fitar da takardun kudin lantarki na N1.502tr a cikin watanni shida, sun kuma iya karbar kusan 80% cikin dari na adadin kudin.

Kara karanta wannan

Jamhuriyar Nijar ta faɗi ƙasashen da take zargi da yunkurin yi mata juyin mulki

Yadda aka karbi kudin wuta a Najeriya
Kudi wuta da aka karba a Najeriya cikin wata 6 | Hoto: GettyImages
Source: Getty Images

Hakan ya haifar da giɓin N301bn, wanda ya yi daidai da kashi daya cikin biyar na gaba daya kudin lantarkin da aka caje abokan hulda a lokacin.

Samun kudin shiga ya sha bamban a watanni

Tattara kudin lantarki ya kai kololuwa a watan Mayu inda aka samu N208.15bn kafin ya ragu zuwa N191.86bn a watan Yuni, wanda shi ne watan da aka fi samun karancin kudi a farkon shekarar.

A watan Janairu an tara N204.74bn, watan Fabrairu N196.68bn, watan Maris N196.13bn, yayin da watan Afirilu aka samu N203.61bn.

A tsakanin kamfanonin 11, Ikeja Electric da Eko DisCo ne suka jagoranci sauran inda kowannensu ya tara N227.56bn.

Abuja DisCo ta samu N215.12bn, Ibadan DisCo N124.47bn, Benin DisCo N99.89bn, sai kuma Port Harcourt DisCo da ke da N97.79bn.

Enugu DisCo ta tara N89.14bn, Kano DisCo N48.91bn, Jos DisCo N39.38bn, yayin da Kaduna DisCo ta samu N30.93bn. Yola DisCo ce ta fi kowa karancin kudin da ta tara da adadin N19.83bn.

Kara karanta wannan

Naira ta yi tashin da ba a taba gani ba a cikin shekaru 2 a kasuwa

Bangare bashi da kudin da ake bi

A bangaren bashin da ba a biya ba, Abuja DisCo ce ke dauke da mafi nauyin bashi na N46.79bn, sai Kano DisCo mai N40.36bn da Ibadan DisCo mai N35.54bn.

Kaduna DisCo tana bi bashin N32.36bn, Enugu DisCo N31.33bn, sannan Jos DisCo N29.98bn.

Eko DisCo ta rubuta bashin N24.35bn, Ikeja DisCo N22.29bn, Port Harcourt DisCo N18.29bn, Benin DisCo N12.53bn, sai Yola DisCo mai N7.96bn na bashin da ake binta.

Kaduna da Kano da Jos sun gaza a karbar kudi

Rahotannin na NERC sun kalubalanci kamfanoni uku saboda raunin da suka nuna wajen tattara kudin lantarki a cikin watanni shida na shekarar.

Kaduna DisCo ta iya karbar 48% ne kacal na kudin da ta caji abokan cinikayya, inda ta tara N30.93bn daga cikin N63.29bn da ta fitar wa abokan cinikinta.

Kano DisCo ta danyi dama-dama kadan, inda ta samu %54.79 cikin dari bayan ta tara N48.91bn daga cikin N89.27billion.

Kara karanta wannan

Pantami ya ci zaben gwamnan Gombe na gwaji da aka yi a intanet

Jos DisCo kuwa ta tara 56.78% cikin dari, inda ta maido da N39.38bn daga cikin N69.36bn na takardun kudin da ta rabar.

'Yan Najeriya dai na ci gaba da kuka kan yadda farashin wutar lantarki ke kara tashi duk da ba a cika samun wutar ba a yankuna da yawa na kasar.

Sauyin da Bankin Duniya ke son kawowa

A wani labarin, Bankin Duniya ya ce zai sauye-sauyen tsarin harajin wutar lantarki da tallafin gwamnati a Najeriya domin samar da wadataccen kudi a bangaren wutar lantarki.

Bankin ya bayyana hakan ne a cikin tsarin hadin gwiwar kasashe na shekaru shida da ya tsara wa Tarayyar Najeriya daga kasafin kudin shekarar 2026 zuwa 2032.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng