Najeriya Ta Fada wa Majalisar Dinkin Duniya Gaskiya kan ‘Mallakar’ Makamin Nukiliya

Najeriya Ta Fada wa Majalisar Dinkin Duniya Gaskiya kan ‘Mallakar’ Makamin Nukiliya

  • Jakadan Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce Najeriya ba ta mallaki makaman nukiliya ba
  • Jimho Ibrahim ya bukaci a sake duba dokar Majalisar Dinkin Duniya kan rashin tsoma baki idan ƙasa na gwajin makaman nukiliya
  • Ya ce Najeriya na haɗin gwiwa da ƙasashe daban-daban wajen ƙarfafa ƙoƙarin duniya na kawar da gwajin makaman nukiliya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jakadan Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya magantu kan zargin mallakar makamin nukiliya.

Jimoh Ibrahim ya bayyana wa Najeriya ba ta mallaki makaman nukiliya ko makaman kare dangi.

Najeriya ta musanta batun mallakar makamin nukiliya
Shugaba Bola Tinubu yana jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Ibrahim ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a gaban Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya a taron cikakken zama na 108, cewar Channels TV.

Taron na cikin zaman karo na 80 na Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya, wanda aka gudanar a birnin New York.

Kara karanta wannan

Atiku ya ragargaji Tinubu kan tafiya hutu Turai 'Najeriya na ci da wuta'

Martanin Najeriya kan zargin shirin mallakar nukiliya

Ya ce Najeriya ba ta taɓa bin wata hanya ko shirin samar da makaman nukiliya ba, tare da sake tabbatar da matsayinta na kawar da gwaje-gwajen makaman nukiliya.

Ibrahim, wanda kuma shi ne shugaban Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan Kasafi da Gudanarwa, ya bukaci a sake duba Mataki na 2(7) na Yarjejeniyar Majalisar.

Ya yi hujjar cewa ka’idar rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gida bai kamata ta hana kasa da kasa daukar mataki kan kasashen da ke gwada makaman nukiliya ba.

Ya kuma ce bai kamata ka’idar ta hana daukar mataki kan kasashen da ke mallakar makaman kare dangi, saboda barazanar da irin wadannan makamai ke haifarwa.

Jakadan Najeriya ya bayyana matsayin Shugaba Bola Tinubu, inda ya ce Najeriya na da muhimman hukumomi da hanyoyin sa ido kan batutuwan da suka shafi makaman kare dangi.

Ya bayyana Hukumar Makamashin Nukiliya ta Najeriya a matsayin daya daga cikin muhimman hukumomin da ke kula da harkokin nukiliya da tsarin sa ido.

Kara karanta wannan

'Matsala ne dawo da tallafin mai': Malamin Musulunci ya gargaɗi ƴan siyasa kan kamfe

Sanata Jimoh ya fayyace gaskiya kan mallakar nukiliya a Najeriya
Jakadan Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Jimoh Ibrahim. Hoto: House of Representatives.
Source: Facebook

Hadin kan da Najeriya ke ba kasashen duniya

A cewar Ibrahim, Najeriya na aiki tare da kasashe daban-daban a duniya, ciki har da Rasha, China, Faransa, Koriya ta Kudu da Amurka.

Ya ce Shugaba Tinubu ya umarce shi da ya sake tabbatar da shirye-shiryen Najeriya na karfafa hadin gwiwar duniya wajen kawar da gwajin makaman nukiliya.

Ibrahim ya ce Najeriya ta goyi bayan bayanin da Kungiyar Afirka ta gabatar a taron Majalisar Dinkin Duniya kan batun makaman nukiliya.

Ya kuma taya kasashen duniya murnar cikar shekaru 30 da rattaba hannu kan Yarjejeniyar Hana Gwajin Makaman Nukiliya ta Kowane Iri.

Ya bayyana cewa Afirka na ci gaba da kasancewa yankin da ba a yarda da makaman nukiliya ba, tare da kin amincewa da gwajin makaman nukiliya.

Jakadan ya bukaci kasashen duniya su ci gaba da kokarin kawar da gwajin makaman nukiliya, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen samar da duniya mafi aminci.

Kara karanta wannan

'Akwai gagarumar matsala': Malamin addini ya bukaci Tinubu ya hakura da takara

Ya ce dakatar da irin wadannan gwaje-gwaje na da matukar muhimmanci wajen kare duniya daga barazanar da makaman nukiliya ke haifarwa, cewar Sahara Reporters.

Ibrahim ya kuma taya kasashen Majalisar Dinkin Duniya murnar ci gaban da aka samu cikin shekaru 30 wajen yaki da gwajin makaman nukiliya.

Tinubu ya karyata shirin makamin nukiliya

An ji cewa gwamnatin tarayya karkashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta ce ba ta da shirin ƙerawa ko gwajin makaman nukiliya.

Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ne ya faɗi matsayar Najeriya da ya karbi bakuncin shugaban kungiyar CTBTO a Abuja.

Wannan dai na zuwa ne bayan yakin da ya auku na tsawon kwanaki 12 tsakanin Iran da Isra'ila, wanda ya samu asali daga shirin kera nukiliya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.