"Duk Wanda Ya San Mustapha"; Kwamishinan Abba Ya Yi Fallasa kan Yaron Kwankwaso Mai Takara a 2027
- Mai magana da yawun bakin gwamnan Kano kuma kwamishinan yada labarai ya yi magana kan Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso
- Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewa yaron na Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai da cancantar samun jagoranci
- Kwamishinan ya tabo batun cewa dan takarar mataimakin gwamnan na jihar Kano na jam'iyyar NDC a zaben 2027, bai da cikakkiyar lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Sabon kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya yi maganganu kan madugun Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Sanusi Bature ya kuma yi magana kan yaron Kwankwaso, Mustapha Rabiu Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar mataimakin gwamnan Kano na jam'iyyar NDC a zaben 2027.

Source: Facebook
Kwamishinan yada labaran ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin Gabon Talk Show wanda aka sanya wani bangare na ta a Youtube ranar Lahadi, 8 ga watan Nuwamban 2026.
Me Sanusi Bature ya ce kan Mustapha Kwankwaso?
Sanusi Bature ya bayyana cewa duniya ta san Mustapha Kwankwaso ba mutum ba ne wanda ya cancanci samun jagoranci.
Kwamishinan ya bayyana cewa hatta mahaifinsa ya san cewa bai dace ya samu ragamar jagoranci ba, saboda ba shi abin da ya fi bukata ba.
Hakazalika, ya nuna cewa duk wanda ba wanda zai fara kuka idan Mustapha ya samu kujerar gwamna, fa ce mahaifinsa madugun Kwankwasiyya.
"Da duniya da wanda ya san Mustapha, da wanda ya yi mu'amala da Mustapha, da mu da mu kasan Mustapha, da 'yan uwan Mustapha, da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya san cewa Mustapha ba wanda za a iya ba jagoranci ba ne.
"Mustapha abin da yake bukata, Mustapha gyara hali yake bukata. Babu wani fitaccen gidan gyara hali a duniya da Kwankwaso bai kai Mustapha ba.
"Babu wani fitaccen gidan gyara hali a Najeriya da Kwankwaso bai kai Mustapha ba. Saboda Mustapha, Kwankwaso ya kirkiro reformative ta Kiru.
"Da Allah zai ƙaddara yau a ce ga Mustapha Rabiu Kwankwaso a kujerar Gwamnan Kano, Na rantse da Allah, Sanata Rabiu Kwankwaso ne zai fara ɗora hannu a kai ya yi kuka.”
- Hon. Sanusi Bature Dawakin Tofa
Ya ce shi ba yaron Kwankwaso ba ne
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa shi ba yaron madugun Kwankwasiyya ba ne duk da cewa ya kasance a cikin tafiyar.
Ya bayyana cewa shi yaron mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf ne, wanda shi ne mai magana da yawun bakinsa.
"Ni ba yaron Kwankwaso ba ne, ni yaron yaron Kwankwaso ne. Ni yaron Gwamna Abba Kabir Yusuf ne." In ji shi.

Source: Facebook
Nadamar Kwankwaso kan zaben 2023
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana nadamarsa kan ƙin amincewa da haɗa kai da Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Rabiu Kwankwaso yake takarar mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar NDC a 2027, ya ce da ya fahimci Obi sosai a wancan lokaci, da sun yi haɗin gwiwa sun kayar da jam’iyyar APC.
Asali: Legit.ng

