Sarkin Musulmi Ya Fito da Maganar Gaskiya kan Almajiranci a Arewa
- Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce yawancin yara almajirai na son zuwa makaranta amma talauci ya hana su samun damar yin hakan
- Ya yi gargaɗin cewa ƙaruwar yaran da ba sa zuwa makaranta na iya yin illa ga tsaron ƙasa da ci gabanta
- Sarkin ya yaba wa Gwamnatin Jihar Gombe kan kafa makarantar da ke haɗa karatun Alƙur’ani da ilimin zamani da koyon sana’o’i
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa talauci ne babban dalilin da ke tilasta wa yara almajirai yawo kan tituna suna bara domin samun abinci.
Sarkin Musulmin ya ce yawancin yaran na da sha'awar neman ilimi, amma rashin kuɗi da sauran abubuwan more rayuwa na hana su samun damar zuwa makaranta.

Source: Getty Images
Talauci ne ke tilasta wa yara almajirai bara

Kara karanta wannan
Rashin imani: Yadda 'yan bindiga suka kona mutum 12 'yan gida 1 da ransu a Zamfara
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a birnin Gombe yayin babban taron shekara-shekara na 2026 na ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Makarantar Barewa (BOBA), inda shi ne ya jagoranci taron, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Mai alfarma Sarkin musulmin ya yi kira ga gwamnatoci da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta magance matsalar talauci da ƙaruwar yaran da ba sa zuwa makaranta a faɗin Najeriya.
Ya ce yawancin yaran da ake gani suna yawo kan tituna suna neman abinci ba wai sun ƙi neman ilimi ba ne, illa dai talauci ne ya hana su damar yin hakan.
Sarkin Musulmin ya ce Musulunci bai amince da bara ba, don haka ya kamata kowa ya haɗa kai wajen yaƙi da wannan ɗabi'a.
Wane gargadi Sarkin musulmi ya yi?
Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana cewa ƙaruwar yaran da ba sa zuwa makaranta babbar matsala ce da za ta iya shafar tsaron ƙasa da ci gabanta.
Ya jaddada cewa ilimi muhimmin ginshiƙi ne a koyarwar Musulunci, don haka bai kamata a yi watsi da shi ba saboda yanayin tattalin arzikin iyalin yaro.
A cewarsa, dan Adam na buƙatar ilimi domin ya san yadda zai gudanar da ibadarsa ga Allah Maɗaukakin Sarki, wanda ya halicce shi domin ya bauta masa.
Sarkin ya kuma yi watsi da wasu ra'ayoyi da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa Musulmi ba sa son 'ya'yansu su yi karatu.
Ya yaba wa Gombe kan makarantar almajirai
Ya yaba wa Gwamnatin Jihar Gombe bisa kafa makarantar da ke ba yaran almajirai damar haɗa karatun Alƙur'ani da ilimin zamani, tare da koyon sana'o'i.
Ya kuma kawo misalin irin wannan shiri da ake gudanarwa a Jihar Zamfara, inda ya buƙaci sauran jihohi su yi koyi da waɗannan matakai.
A cewarsa, makarantu da cibiyoyin da ake da su a yanzu ba su wadatar ba idan aka yi la'akari da yawan yaran da ba sa samun damar zuwa makaranta.

Source: Facebook
Tinubu ya yabawa Sarkin musulmi
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai girma Bola Tinubu, ya taya mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, murnar cika shekaru 20 a kan karagar mulki.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin sakon taya murna da ya aika wa Sarkin Musulmin, inda ya yaba da yadda ya jagoranci masarautar cikin shekarun da suka gabata.
Asali: Legit.ng
