'Za a Cika 30,' Sultan Ya Fitar da Sanarwa bayan Duba Watan Jumada Sani

'Za a Cika 30,' Sultan Ya Fitar da Sanarwa bayan Duba Watan Jumada Sani

  • Sarkin Musulmi ya sanar da cewa Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026, ita ce ranar farko ta watan Jumada Sani na shekarar 1448 bayan hijira
  • Fadar Sarkin Musulmi ta ce ba a samu rahoton ganin jinjirin watan Jumada Sani daga kwamitocin duban wata a sassan Najeriya ba a ranar Litinin
  • Ranar Talata, 10 ga Nuwamba, za ta zama ranar cika kwana 30 na watan Jumadal Ula, kamar yadda sanarwar fadar ta bayyana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya sanar da cewa Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026, ita ce ranar farko ta watan Jumada Sani na shekarar 1448 bayan hijira.

Sanarwar da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya fitar a ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, ta ce kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na majalisar, tare da kwamitin duban wata na ƙasa, ba su samu rahoton ganin jinjirin watan ba.

Kara karanta wannan

Barayi sun shiga masallaci sun sace fankoki sama da 20 a Kano

Mai alfarma Sarkin Musulmi
Mai alfarma Sarkin Musulmi a hagu da wata a dama. Hoto: JNI|Getty Images
Source: UGC

Legit ta tattaro bayanai game da sanrwar ne a wani sako da fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ta wallafa a shafinta na Facebook.

Ba a ga watan Jumada Sani ba

Sanarwar ta bayyana cewa kwamitocin duban wata a sassan ƙasar ba su gabatar da wani rahoto da ke tabbatar da ganin jinjirin watan Jumada Sani a ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026 ba.

Kwamitin ganin watan ya bayyana cewa ranar ta yi daidai da 29 ga watan Jumadal Ula na shekarar 1448 bayan hijira.

Jumada Ula zai yi kwana 30

Saboda rashin samun rahoton ganin wata, sanarwar ta ce Talata, 10 ga Nuwamba, za ta zama ranar 30 ga watan Jumada Ula.

Hakan na nufin za a kammala watan Jumadal Ula da kwanaki 30 kafin fara sabon watan Jumada Sani a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, CFR, mni, wanda kuma shi ne shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya amince da rahoton kwamitin.

Kara karanta wannan

Tashar ruwa 1 da shugabannin Najeriya 3 suka amince da gina ta amma har yanzu ba a gama ba

Bisa haka ne ya ayyana Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026, a matsayin ranar farko ta watan Jumada Sani na shekarar 1448 bayan hijira.

Mai alfarma Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi a wajen wani taro. Hoto: JNI
Source: Facebook

Majalisar masarautar Sokoto na aiki tare da kwamitin duban wata na ƙasa wajen tattara rahotannin ganin jinjirin wata daga sassa daban-daban na ƙasar a kowane karshen wata a tsawon shekara a Najeriya.

Magana kan almajiranci a Arewa

A wani rahoto da ya gabata, Sarkin Musulmi ya bayyana cewa talauci da rashin tallafin yau da kullum na daga cikin manyan dalilan da ke sa yaran almajirai a Arewacin Najeriya yawo kan tituna suna bara maimakon samun damar karatu.

Ya bayyana haka ne yayin taron shekara-shekara da aka gudanar a jihar Gombe karkashin kungiyar tsofaffin daliban makarantar Barewa College da ke jihar Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido sun hallara wajen taron da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng