Sheikh Pantami Ya Saka Ranar Shiga Gombe don Fara Kamfen da Gaske
- Bayan hukumar INEC ta sanya sunan dan takarar gwamnan Gombe a karkahin jam'iyyar PDP, Sheikh Isa Ali Pantami, zai shiga jihar fara kamfen
- Pantami ya yi godiya ga jama'ar Gombe da suka yi tsayuwar daka suna masa addu'o'i domin ganin ya samu nasara a rikita-rikitar da aka yi
- Ya bayyana cewa zai shiga jihar Gombe a makon nan domin kara yi wa jama'a godiya da kuma halartar babban taron PDP da za a gudanar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Yayin da ake cigaba da kamfen a Najeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya sanar da cewa zai shiga jihar Gombe domin kaddamar da yakin neman zabe.
Pantami ya bayyana haka ne 'yan kwanaki bayan hukumar zabe ta kasa (INEC) ta maido sunan shi cikin 'yan takara a shafinta.

Source: Facebook
Legit Hausa ta gano cewa dan takarar ya sanar da matakin ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin.
Pantami ya yi wa jama'a godiya
A bidiyon da ya fitar, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi wa jama'ar jihar Gombe da wasu yankunan Najeriya godiya bisa addu'o'in da suka masa.
Mutane da dama sun gabatar da salloli da addu'o'i domin rokon Allah ya sa a mayar da sunan Malam cikin 'yan takara a shafin INEC.
Magoya bayan Pantami sun yi salla suna rokon Allah ne bayan a fitar da sunayen 'yan takarar gwamna ba tare da ganin sunan shi ba a karon farko.
Pantami ya ce:
'Allah ya karbi addu'o'in da aka yi. 'Yan uwa da suka rika addu'o''i muna godiya a gare ku,'
Pantami zai shiga Gombe
Bayan godiya, Pantami ya bayyana cewa zai shiga jihar Gombe daga Abuja karkashin jagorancn Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo domin godiya ga jama'a.

Kara karanta wannan
Kamfanin simintin Ashaka ya kulla yarjejeniyar cigaban al'umma na shekaru 5 da Funakaye
Ya ce ranar 11 ga Nuwamban 2026 zai shiga jihar Gombe domin godewa jama'a, inda ya bukaci dukkan magoya bayan tafiyar su fito su tarbe su.
Ya bayyana cewa za a fitar da cikakkiyar sanarwa game da taron da za su yi a ranar Laraba, 11 ga Nuwamba a lokaci na gaba.

Source: Facebook
A cikin bayanin da dan takarar ya yi, ya bayyana cewa za a kaddamar da kwamitin yakin neman zaben da jam'iyyar PDP za ta jagoranta a jihar Gombe.
Ya kara da cewa jam'iyyar na gayyatar kowa da kowa, 'yan takara da sauran 'yan jam'iyya domin halartar gagarumin taron da za su yi.
'Yan PDP sun koma APC
A wani labarin, kun ji cewa wasu shugabannin jam'iyyar PDP a jihar Gombe sun koma jam'iyyar APC mai mulki yayin da ake tunkarar zabe.
Bayanin da gwamnatin jihar ta yi ya nuna cewa daga cikin wadanda suka sauya sheka akwai shugaban PDP ana karamar hukumar Nafada.
Haka zalika Legit Hausa ta gano cewa sauran shugabannin da suka sauya sheka akwai jagororin PDP na Kwami da Yamaltu Deba.
Asali: Legit.ng
