Shugaban APC Ya Fito da Magana kan Batun Tinubu Bai da Lafiyar Tsayawa Takara a 2027

Shugaban APC Ya Fito da Magana kan Batun Tinubu Bai da Lafiyar Tsayawa Takara a 2027

  • Nentawe Yilwatda ya yi watsi da damuwar da ake nunawa kan lafiyar Tinubu, yana mai cewa shugaban ƙasar yana da ƙoshin lafiyar da zai iya tsayawa takara
  • Shugaban APC ya ce rashin halartar Tinubu wasu tarukan yaƙin neman zaɓe ba yana nufin gazawa ko rashin ƙarfin jagoranci ba ne
  • Yilwatda ya kare tikitin Musulmi da Musulmi na Tinubu da Kashim Shettima, yana mai cewa Kiristoci na samun damar bayyana ra'ayoyinsu a gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya yi watsi da damuwar da ake nunawa kan lafiyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin babban zaɓen 2027.

Yilwatda ya dage cewa shugaban ƙasar yana da ƙoshin lafiyar da zai iya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa, tare da kira ga ’yan Najeriya da kada su ɗauki wasu kalaman rashin goyon baya a matsayin alamar cewa jama'a da dama ba sa son Tinubu.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Wike zai raba biliyoyi don tabbatar da tazarcen Tinubu

Nentawe ya yi magana kan lafiyar Tinubu
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Facebook

Yilwatda ya ce Tinubu yana da ƙoshin lafiya

Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamban 2026.

Ya kuma yi magana kan yadda Tinubu ba ya halartar wasu tarukan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, inda ya ce ba zai yiwu shugaban ƙasa ya halarci dukkan tarukan ba yayin da yake gudanar da ayyukan da kundin tsarin mulki ya ɗora masa.

Shugaban APC ya bayyana cewa wasu jami'an gwamnati sun samu shawarar halartar zaɓaɓɓun tarukan yaƙin neman zaɓe maimakon zuwa dukkan wuraren da aka shirya, domin kada ayyukan gwamnati su samu tangarda.

Ya kare rashin halartar Tinubu tarukan kamfe

Bayan da Tinubu ya bayyana a baya cewa ba zai halarci dukkan tarukan yaƙin neman zaɓe ba saboda nauyin da ke kansa na shugabancin ƙasa, Yilwatda ya ce bai kamata a fassara hakan a matsayin rauni ko rashin iya jagorantar jam'iyyar ba.

Kara karanta wannan

Tsohon abokin takarar Buhari ya bayyana dalilin kin karbar tayin mukamin da Tinubu ya yi masa

A cewarsa, akwai buƙatar shugaban ƙasa ya daidaita ayyukan gwamnati da harkokin yaƙin neman zaɓe, musamman ganin cewa yana da nauyin gudanar da mulkin ƙasar.

Ya kuma jaddada cewa rashin halartar wasu taruka ba zai hana Tinubu jagorantar ƙoƙarin APC na neman sake lashe zaɓen shugaban ƙasa ba.

Yilwatda ya kare tikitin Musulmi da Musulmi

A wani ɓangare na jawabin nasa, shugaban APC ya kare tikitin takarar shugaban ƙasa na Musulmi da Musulmi da Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, suke kai wa zaɓen 2027.

Yilwatda ya yi watsi da damuwar cewa tsarin zai iya tauye haƙƙin Kiristoci a gwamnatin APC, yana mai cewa muryoyinsu na samun damar bayyana a harkokin gwamnati.

Ya ce Kiristocin da jam'iyyar ta tattauna da su sun nuna gamsuwa da tsarin tikitin, duk da cewa tun farko wasu na fargabar cewa hakan zai rage tasirinsu wajen yanke shawarar gwamnati.

Nentawe ya kare shugaban kasa Bola Tinubu
Farfesa Nentawe Yilwatda na jawabi a wajen kamfen din APC Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Facebook

ADC ta ragargaji APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar ADC ta kalubalanci APC mai mulki da ta gwada ƙarfin farin jininta a rumfunan zaɓe, maimakon amfani da shari’o’in kotu wajen hana ta shiga zaɓen 2027.

Ta ce idan APC ta amince tana da ƙarfin lashe zaɓe, to ya kamata ta bari a gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci, ba tare da tsoratarwa ko hana wasu shiga fafatawar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng