Masu Tallata Tinubu Gida Gida za Su Shiga Zamfara da Wasu Jihohi 7
- Kungiyar PBAT Door-to-Door Movement mai goyon bayan Shugaba Bola Tinubu ta ce za ta je kamfen ɗin wayar da kan jama’a zuwa wasu jihohi takwas
- Rahoto ya nun a cewa jihohin da za a ziyarta sun haɗa da Enugu, Zamfara, Jigawa, Anambra, Kebbi da Abia da sauransu
- Kungiyar ta ce ta kai ayyukan wayar da kan jama’a zuwa kusan jihohi 20, tare da raba motoci sama da 500 domin ƙarfafa ayyukanta a faɗin ƙasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Kungiyar PBAT Door-to-Door Movement, wadda Tompolo, ya kafa, ta sanar da shirin zuwa kamfen ɗin tallata Shugaba Bola Tinubu zuwa wasu jihohi takwas tsakanin 9 zuwa 14 ga Nuwamba, 2026.
Kungiyar ta bayyana cewa ziyarar za ta shafi jihohin Enugu, Cross River, Bayelsa, Zamfara, Jigawa, Anambra, Kebbi da Abia, kamar yadda jadawalin da ta fitar ya nuna.

Kara karanta wannan
“Ko zai shafi Tinubu a 2027?” Yadda al’ummar Legas suka tarbi Kwankwaso ya ja hankali

Source: Facebook
Jihohin da kungiyar za ta ziyarta
A cewar jadawalin, te Cable ta rahoto cewa kungiyar za ta fara rangadin ne a ranar Litinin, inda za ta gudanar da taruka a jihohin Enugu da Cross River.
A jihar Enugu, za a gudanar da taron ne da ƙarfe 10:00 na safe a filin Okpara Square, yayin da za a yi na Cross River da ƙarfe 2:00 na rana a Calabar Municipal Field.
A ranar Laraba kuma, tawagar za ta je jihar Bayelsa, inda za ta gudanar da taro da ƙarfe 10:00 na safe a filin wasa na Siasia Stadium da ke Yenagoa.
Yadda kamfen din zai gudana a Arewa
Kungiyar ta tsara gudanar da taro a jihar Zamfara ranar Alhamis da ƙarfe 11:00 na safe, sannan ta wuce jihar Jigawa domin wani taro da ƙarfe 2:00 na rana.
A ranar Juma’a, za a gudanar da taruka a jihohin Anambra da Kebbi da ƙarfe 10:00 na safe da 2:00 na rana, bi da bi.

Kara karanta wannan
Abubuwan da ya kamata ku sani game da tallafin N50,000 da aka fara turawa mutane a Najeriya
Za a kammala rangadin ne a jihar Abia ranar Asabar da ƙarfe 10:00 na safe. Sai dai kungiyar ba ta bayyana wuraren da za a gudanar da tarukan a jihohin Zamfara, Jigawa, Anambra, Kebbi da Abia ba.

Source: Facebook
Motoci 500 da kungiyar ta raba
The Nation ta wallafa cewa kungiyar ta bayyana cewa zuwa yanzu ta kai ayyukan wayar da kan jama’a zuwa kusan jihohi 20 na Najeriya.
Ta ce ta kuma raba motoci sama da 500 domin taimaka wa masu gudanar da ayyukanta da masu kula da harkokinta a sassa daban-daban na ƙasar.
A cewarta, motocin za su taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirga da daidaita ayyukan masu gudanar da kamfen, domin su iya isa ga al'ummomi, kasuwanni da unguwanni.
Akpabio zai samawa Tinubu kuri'u
A wani labarin, mun ruwaito cewa Godswill Akpabio, ya yi alkawarin cewa jihar Akwa Ibom za ta samar wa Shugaba Bola Tinubu kuri'u sama da miliyan biyu.
Gwamnan jihar, Umo Eno, da sarakunan gargajiya sun sake tabbatar da goyon bayansu ga shugaba Tinubu yayin ziyarar da ya kai jihar.
Akpabio ya bayyana Tinubu a matsayin jagora mai hangen nesa, tare da cewa ’yan majalisa za su ci gaba da mara wa gwamnatinsa baya.
Asali: Legit.ng