Tinubu Ya Nada Olukoyede Sabon Shugaban Hukumar EFCC

Tinubu Ya Nada Olukoyede Sabon Shugaban Hukumar EFCC

  • A karshe, Shugaba Tinubu ya nada Ola Olukoyede a matsayin sabon shugaban Hukumar EFCC
  • Olukoyede ya shafe shekaru fiye da 22 a hukumar kuma ya kasance kwararren lauya masanin makaman aiki
  • Hadimin Tinubu a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya tabbatar da nadin a yau Alhamis 12 ga watan Oktoba

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya nada sabon shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci (EFCC) bawan dakatar da Abdulraheed Bawa a matsayin shugaban EFCC.

Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka a yau Alhamis 12 ga watan Oktoba a Abuja, Legit ta tattaro.

Tinubu ya nada sabon shugaban Hukumar EFCC
Tinubu Ya Nada Olukayede Shugaban Hukumar EFCC. Hoto: @Imranmuhdz, @officialBAT.
Asali: Twitter

Waye Tinubu ya nda shugaban EFCC?

A cikin sanarwar, Ngelale ya ce an nada Ola Olukoyede wanda lauya ne a matsayin sabon shugaban hukumar.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Jawo Yaron Aminin Buhari, Ya ba Shi Mukami Mai Tsoka a Gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ola ya na da makamar sanin aiki har na tsawon shekaru 22 a hukumar wanda kuma kwararre ne a bangaren shari'a.

Har ila yau, Bola Tinubu ya sake nada sabon sakataren hukumar, Muhammad Hassan Hammajoda Daily Trust ta tattaro.

Wannan nadin na Olukoyede na zuwa ne bayan dakatar da tsohon shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa.

Wasu nade-nade kuma Tinubu ya yi a EFCC?

Ana sa ran zai jagoranci hukumar har na tsawon shekaru hudu wanda shugaban kasa na da hurumin kara masa wani wa'adin.

Sabon sakataren hukumar, Hammajoda zai yi wa'adin shekaru biyar, dukkan wadannan nade-nade sun ta'allaka ne da tantance su da majalisar Dattawa za ta yi.

Sanarwar ta ce:

"Shugaba Tinubu ya nada sabbin shugabannin hukumar EFCC wanda ya aminta da kwazonsu don dakile matsalar cin hanci a kasar.

Kara karanta wannan

Jerin Manyan Jami'an Gwamnati 3 Da Tinubu Ya Kora Yayin Da Ya Ke Nada Masu Maye Gurbinsu

"Shugaban ya himmatu wurin kawo karshen cin hanci wanda na daga cikin kudurinsa tun kafin hawa karagar mulki."

Olukoyede ya

Tinubu ya yi sabbin nade-nade a hukumomin NCC, NIPOST

A wani labarin, Shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da nadin shugabannin hukumomin NCC da NIPOST da kuma NITDA.

Hadimin shugaban ta fannin yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka a jiya Laraba 11 ga watan Oktoba a Abuja.

Ajuri ya ce dukkan sabbin nade-naden da aka yi za su kasance karkashin ma'aikatar sadarwa da kirkire na zamani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel