Ma'aikatan Hukumar EFCC 40 Sun Jawo Wa Kansu Matsala a Wurin Aiki

Ma'aikatan Hukumar EFCC 40 Sun Jawo Wa Kansu Matsala a Wurin Aiki

  • EFCC ta kori sama da ma’aikata 40 cikin shekaru biyu da rabi saboda zargin cin hanci da rashawa da almundahana
  • Shugaban EFCC Ola Olukoyede ya ce sama da mutum biyar daga cikin waɗanda aka kora suna fuskantar shari’a a kotu
  • Hukumar ta kuma ce ta gano N288.1bn a matsayin harajin da aka kwato wa gwamnatin tarayya da jihohi ta hanyar aiwatar da dokoki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja – Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta bayyana cewa ta kori sama da ma’aikatanta 40.

Hukumar EFCC ta kori ma'aikatan ne cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata saboda zargin cin hanci da rashawa da sauran laifukan kuɗi.

EFCC ta kori wasu ma'aikatanta
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede na magana da manema labarai Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, 31 ga watan Agustan 2026 yayin wani taro da ya yi da shugabannin kafafen yaɗa labarai da ‘yan jarida a Abuja, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

A karshe, an gano wanda ya kashe mawakin duniya Tupac Shakur

Wasu daga cikin ma’aikatan na fuskantar shari’a

Olukoyede ya ce fiye da biyar daga cikin ma’aikatan da aka kora a halin yanzu suna fuskantar shari’a kan zargin aikata laifukan da suka saɓa wa doka.

Ya ƙara da cewa ana shirya takardun shari’ar wasu ma’aikatan da ake zargi da aikata irin waɗannan laifuka domin gurfanar da su a gaban kotu.

Shugaban EFCC ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin hukumar na tabbatar da cewa jami’anta suna bin ƙa’idodin gaskiya da riƙon amana yayin bincike da gurfanar da masu aikata laifukan cin hanci da rashawa.

EFCC ta ƙara tsaurara dokar karɓar kyaututtuka

Olukoyede ya bayyana cewa hukumar ta kuma ƙaddamar da wasu matakai domin ƙarfafa gaskiya da ɗaukar alhaki tsakanin ma’aikatanta, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.

Daga cikin matakan akwai sabuwar dokar karɓar kyaututtuka da za ta tsara irin kyaututtukan da jami’an EFCC za su iya karɓa da kuma yadda za su bayyana su.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya kawo sabon rikici a ADC kan yadda Atiku ke sukar Tinubu

Ya ce ma’aikata za su rika bayyana kadarori ko kyaututtukan da suka karɓa waɗanda suka haura wani ƙayyadadden ƙima, ciki har da kyaututtukan da ‘yan uwansu da ke ƙasashen waje suka turo musu.

A cewarsa, hukumar za ta fayyace nau’o’i da ƙimar kyaututtukan da ma’aikata za su iya karɓa domin tabbatar da cewa za su iya bayyana tushen dukiyar da salon rayuwarsu.

Shugaban EFCC ya gargadi jami’an hukumar cewa ba za su iya yaƙar cin hanci da rashawa yadda ya kamata ba idan su kansu suna aikata irin laifukan.

EFCC ta kwato N288.1bn na haraji

A wani ɓangare, Olukoyede ya ce ayyukan EFCC na yaƙi da cin hanci da rashawa sun taimaka wajen ƙara samun kuɗaɗen shiga ga gwamnati.

Ya bayyana cewa hukumar ta kwato kusan N288.1bn na haraji daga gwamnatin tarayya da kuma jihohi a lokacin da ake magana a kai.

Ya ce daga cikin kuɗin akwai N173.2bn da aka kwato wa gwamnatin tarayya, yayin da N114.9bn aka danganta da hukumomin tattara harajin cikin gida na jihohi.

Olukoyede ya jaddada cewa kuɗin da aka samu ba sabon haraji ba ne, illa dai kuɗin da aka kwato ta hanyar tilasta bin wasu wajibai da doka ta riga ta tanada.

Kara karanta wannan

Wani kaya sai amale: Yadda EFCC ta kwato N1.3trn a hannun barayi

EFCC ta kori wasu ma'ikatanta
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

EFCC ta kwato makudan kudade

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin kasa zagon kasa (EFCC) ta bayyana adadin makudan kudaden da ta kwato cikin shekara uku.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa ta kwato N1.23trn da wasu makudan kuɗaɗe na wasu ƙasashe cikin kusan shekaru uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng