TETFund Ta Bude Shafin Tallafin da Aka Ware Wa Naira Biliyan 10, Ta Fadi Yadda Mutane Za su Cike
- Gwamnatin Tarayya ta amince da ware Naira biliyan 10 a zagayen tallafin binciken NRF na 2026 karkashin hukumar TETFund
- TETFund ta ce za a tallafa wa ayyukan bincike a fannoni 30 da aka fi ba fifiko, ta nemi malamai a manyan makarantun gwamnati su cike
- Ann bude shafin neman tallafin a yau 31 ga Agusta, yayin da ranar 15 ga Oktoba, 2026 za ta kasance ranar karshe ta gabatar da takardun neman tallafin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta amince da ware Naira biliyan 10 a zagayen shirin tallafin bincike na NRF na shekarar 2026 karkashin Hukumar Raya Manyan Makarantu (TETFund).
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar neman takardun bayanan bincike da Sonny Echono, shugaban TETFund, ya sanya wa hannu ranar Asabar da ta wuce.

Kara karanta wannan
Tirkashi: Rundunar sojojin Najeriya ta gamu da gagarumar matsala da aka yi mata kutse

Source: Facebook
A rahoton da The Cable ta kawo, ya ce tallafin zai taimaka wajen gudanar da ayyukan bincike a fannoni 30 da aka fi bai wa fifiko.
TETFund ta ce zagayen tallafin na 2026 ya biyo bayan nasarar kammala zagayen na 2025, wanda ya kai ga bayar da tallafin sama da Naira biliyan 6.09 domin ayyukan bincike 174.
Yadda za a nemi tallafin TETFund
A cewar TETFund, samun damar neman tallafin NRF na 2026 zai fara ne da gabatar da takardun bayanan bincike daga manyan masu gudanar da ayyukan binciken da ake son aiwatarwa.
Sai dai manyan masu binciken da aka tantance takardun bayanan ayyukansu kuma aka ga sun cancanci samun tallafi ne kawai za a gayyace su domin gabatar da cikakkun bayanai.
TETFund ta ce malaman manyan makarantun gwamnati a Najeriya ne kadai suka cancanci neman tallafin.
Shafin da za a shiga don cike tallafin
Haka zalika, sanarwar ta bayyana cewa za a gudanar da dukkan tsarin neman tallafin ta yanar gizo.

Kara karanta wannan
EFCC ta kama mutum 2 'yan Najeriya, ta mika su ga Amurka saboda laifin da suka aikata
Ana bukatar masu binciken da suka cancanta su shiga shafin shirin NRF na TETFund (nrf.tetfund.gov.ng), inda za a jagorance su kan yadda za su shirya tare da gabatar da takardun bayanan bincikensu.
An bukaci masu neman tallafin da su karanta bayanan binciken da ka’idojin neman tallafin kafin su gabatar da takardunsu.
Kwamitin tantancewa da sa ido na shirin ne zai tantance dukkan takardun bayanan binciken da aka gabatar kafin ya zsbi wadanda za s ba tallafin, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

Source: Twitter
Fannonin da aka fi bai wa fifiko
TETFund ta ce za a bude shafin cike tallafin shirin bincike na NRF a ranar 31 ga Agusta, 2026 kuma za a rufe gabatar da takardun neman tallafin ranar 15 ga Oktoba, 2026.
An raba fannoni 30 da aka bai wa fifiko zuwa rukuni uku, wanda ya hada da ilimin dan Adam da kimiyyar zamantakewa; kimiyya, injiniyanci, fasaha da kirkire-kirkire; da kuma batutuwan da suka shafi fannoni daban-daban.
Za a tallafa wa yan kasuwa a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa hukumar SMEDAN da kamfanin fasaha na Zoho sun ƙaddamar da wani shirin tallafa wa kananan yan kasuwa 25,000 a Najeriya.
An ruwaito cewa a ƙarƙashin yarjejeniyar, Zoho za ta samar da kuɗin amfani da manhajojinta da darajarsu ta kai har Naira biliyan 20 ga ‘yan kasuwa da suka cancanta.
Asali: Legit.ng