An Jero wa Gwamnan Filato Tambayoyi da Ya Ce Akwai Hisbah a Jihar

An Jero wa Gwamnan Filato Tambayoyi da Ya Ce Akwai Hisbah a Jihar

  • Solomon Dalung ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Plateau da ta bayyana cikakkun bayanai kan zargin da ake yi wa wasu masu gudanar da ayyukan Hisbah a Jos
  • Dalung ya ce bai kamata a mayar da batun zuwa rikicin Kirista da Musulmi ba, ya ce lamarin ya shafi ikon aiwatar da doka a fadin jihar ne
  • Ya bukaci gwamnati ta gudanar da cikakken bincike, ta bayyana waɗanda abin ya shafa da kuma waɗanda suka kafa, dauki nauyin ko tallafa hukumar idan akwaisu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato – Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Plateau da ta fito fili ta bayyana hujjojin zargin ayyukan Hisbah da ta ce an gudanar ba tare da izini ba a Jos.

Kara karanta wannan

Gwamna ya hana ayyukan 'Hisbah' a jiharsa, ya ba jami'an tsaro umarni

Dalung ya ce umarnin da gwamnan jihar ya bayar na dakatar da ayyukan Hisbah da ba a san da su ba bai kamata a mayar da shi wata muhawara tsakanin Kirista da Musulmi ba.

Caleb Mutfwang da Solomon Dalung
Gwamna Caleb Mutfwang a hagu da Solomon Dalung a dama. Hoto: Plateau State Government|Solomon Dalung
Source: Facebook

Dalung ya wallafa a Facebook cewa idan wasu mutane suna tsoratar da mazauna gari, karɓar kuɗi, sanya dokoki ko hana zirga-zirga ba tare da hurumin doka ba, to ya kamata a bayyana su.

Dalung ya nemi a kawo hujjoji

Dalung ya ce akwai wani muhimmin bangare da bai kamata a yi watsi da shi ba, wato nauyin da ke kan gwamnati na tabbatar da zarge-zargen da ta gabatar.

Ya ce zarge-zargen suna da matuƙar muhimmanci, saboda haka gwamnati na da alhakin gudanar da bincike tare da bayyana gaskiyar lamarin ga jama'a.

Ya yi tambayoyi kan inda ƙungiyar take gudanar da ayyukanta, waɗanda abin ya shafa, lokacin da abubuwan suka faru da kuma abin da aka karɓa ko aka tilasta wa jama'a.

Haka kuma, ya nemi a bayyana waɗanda ake zargi, waɗanda suka kafa ƙungiyar, waɗanda suka dauki nauyinta da kuma hujjojin da gwamnati ke da su kan zargin.

Kara karanta wannan

'Matsala ne dawo da tallafin mai': Malamin Musulunci ya gargaɗi ƴan siyasa kan kamfe

Ya nemi a gano 'yan Hisbah

Dalung ya ce idan bincike ya tabbatar da zarge-zargen, ya kamata a gurfanar da waɗanda suka aikata laifin a gaban doka.

Ya ce hukumomi su gano waɗanda suka kafa ƙungiyar, waɗanda suka samar da kuɗin gudanar da ayyukanta, waɗanda suka ƙarfafa ta da kuma waɗanda suka samar mata da kayan aiki ko sauran tallafin da ta yi amfani da shi.

“Idan an tabbatar da zarge-zargen, waɗanda ke da hannu su fuskanci doka. Amma binciken bai kamata ya tsaya kan waɗanda ke aiwatar da umarni ba,”

In ji shi.

Taswirar jihar Filato
Taswirar jihar Filato a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Ya ce Plateau ta kasance gida ga Kiristoci, Musulmi, masu bin addinin gargajiya da kuma waɗanda ba sa bin wani addini, don haka ya kamata doka ta kare kowa ba tare da nuna bambanci ba.

Kirista ya gina masallaci

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani Kirista mazaunin Jihar Plateau, Peter Ibrahim Gyendyeng ya gina Masallacin Juma'a a garin Gana Ropp da ke Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi ta jihar.

Kara karanta wannan

Zargin safarar kwaya: Tinubu ya kawo dalilai 4 ga kotun Amurka kan sakin sirrinsa

Gyendyeng, wanda ya taɓa wakiltar mazabar Barkin Ladi/Bassa a Majalisar Wakilai, ya ce ya gina masallacin ne domin ya zama alamar haɗin kai tsakanin Musulmi da Kiristoci a yankin.

Musulman yankin sun bayyana farin cikinsu kan matakin, suna mai cewa ya nuna yadda za a iya samun fahimtar juna da zama tare tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng