Motar Sojojin Najeriya Ta Gamu da Tsautsayi, Ta Kashe Mutane da Dama a cikin Kasuwa

Motar Sojojin Najeriya Ta Gamu da Tsautsayi, Ta Kashe Mutane da Dama a cikin Kasuwa

  • An ce wasu ’yan kasuwa biyar sun mutu bayan wata motar sojoji kirar Hilux ta kwace wa direba, ta kutsa cikin kasuwa a Chanchangi, jihar Taraba
  • Motar tana rakiyar ’yan kasuwa ne daga Wukari zuwa Takum saboda yawaitar hare-haren ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a hanyar
  • ’Yan kasuwa da dama sun jikkata, yayin da aka kai gawawwaki da wadanda suka samu raunuka Asibitin Janar na Takum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Taraba - Wasu ’yan kasuwa biyar sun rasa rayukansu bayan wata motar sojoji kirar Hilux ta kwace wa direba, ta sfka cikin wata kasuwa a garin Chanchangi da ke karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.

Lamarin ya faru ne ranar Laraba yayin da motar sojojin ke rakiyar wasu ’yan kasuwa daga garin Wukari zuwa Takum saboda yawaitar hare-haren sace mutane a kan hanyar.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Yan bindiga da yawa sun baƙunci lahira a jihar Sakkwato

Sojoji.
Jami'an rundunar sojin Najeriya yayin da suke sintiri don tabbatar da tsaro Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

Wani mazaunin garin, Tony David, ya shaida wa Daily Trust ta wayar tarho cewa motar sojojin na cikin ayarin da ke rakiyar ’yan kasuwar saboda matsalar tsaro da ake fama da ita a yankin.

Ya ce wadanda motar ta murkushe suna cikin ’yan kasuwar da suka shimfida kayayyakin da suke sayarwa a gefen hanya.

Yadda motar sojojin ta kutsa kasuwa

David ya ce motar sojojin ta gamu da hatsari ne yayin da take kan hanyar, lamarin da ya sa ta kutsa cikin wurin da ’yan kasuwar suke gudanar da harkokinsu.

Ya bayyana cewa baya ga wadanda suka mutu, wasu ’yan kasuwa da dama sun samu raunuka sakamakon hatsarin.

A cewarsa, an kai gawawwakin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin Takum domin kula da wadanda suka samu raunuka.

’Yan kasuwa na bukatar kariya

Mazaunin ya ce rakiyar da jami’an tsaro ke yi wa ’yan kasuwa na da alaka da yawaitar hare-haren masu garkuwa da mutane a hanyar da ta hada Wukari da Takum.

Kara karanta wannan

Mummunan hatsarin mota ya lamushe rayukan iyalan tsohon Kwamishina 'baki ɗaya'

Ya bayyana cewa ’yan kasuwar na tafiya ne zuwa Takum a karkashin rakiyar jami’an tsaro domin samun kariya daga yan bindiga.

Taraba.
Taswirar jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

’Yan sanda sun fara bincike

Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar Taraba, ASP Victor Mshelizah, ya ce ya ga wani sako da aka wallafa a kafar sada zumunta game da hatsarin.

Ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan adadin mutanen da suka mutu ko wadanda suka jikkata ba, kamar yadda Leadership ta kawo.

“Na ga wani bayani kan lamarin a wani dandali. Da zarar na samu cikakken bayani daga DPO na Takum, zan tuntube ku,” in ji ASP Mshelizah.

Sojoji sun yi artabu da yan bindiga

Kun ji cewa jami'an tsaro sun yi nasarar fatattakar yan bindiga da suka yi yunkurin kai hari barikin sojoji da ke Sifawa a karamar hukumar Bodinga ta Sakkwato.

Bayanai daga mazauna yankin sun nuna cewa sojoji da yan sanda sun tari maharan, inda suka kashe yan bindiga da dama yayin musayar wuta.

Dakarun Sojoji biyu sun samu raunuka, yayin da ake ci gaba da farmakin sama kan ’yan bindigar da suka tsere cikin dazuzzuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262