Sauro Ya Shiga Turai, Ya Fara Kashe Mutane da Cizo a Jamus
- Rahoto ya ce ma'aikata biyu na filin jirgin saman Frankfurt a kasar Jamus sun mutu bayan kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro
- Rahotanni sun nuna cewa ma'aikata shida ne suka kamu da cutar, yayin da hudu daga cikinsu ke samun sauki bayan an kwantar da su a asibiti
- Hukumomin lafiya sun ce ana zargin wani sauro mai dauke da kwayar cutar ya shigo kasar Jamus a cikin jirgin sama ko kayayyaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Frankfurt, Jamus – Mutane biyu daga cikin ma'aikatan filin jirgin saman Frankfurt, mafi girman filin jirgin sama a kasar Jamus, sun mutu bayan kamuwa da zazzabin cizon sauro.
Hukumomin kula da lafiya da kuma kamfanin Fraport mai kula da filin jirgin saman sun tabbatar da barkewar cutar da ta shafi ma'aikata shida.

Source: Getty Images
The Independent ta wallafa cewa daga cikin mutum shida da suka kamu da cutar, biyu sun mutu yayin da sauran hudu aka kai su asibiti domin samun kulawa, kuma rahotanni sun ce suna samun sauki.
Yadda cutar cizon sauro ta bulla
Hukumomin lafiya sun ce ana zargin cewa wani sauro nau'in Anopheles mai dauke da kwayar cutar zazzabin cizon sauro ne ya shigo kasar ta cikin jirgin sama.
Ana kiran irin wannan lamari da "zazzabin cizon sauro na filin jirgin sama", wanda ke faruwa idan sauro mai dauke da cutar ya yi tafiya a cikin jirgin sama ko kayan dakon kaya.
Sauro kan iya cizon mutane a filin jirgin saman da ya sauka ko kuma yankunan da ke kusa da shi, wanda hakan kan jawo kamuwa da cutar.
An gano masu cutar a watan Yuli
Cibiyar Robert Koch mai kula da yaki da cututtuka a Jamus, ta ce an fara gano mutum hudu da suka kamu da cutar a tsakiyar watan Yuli.
Rahoton ya nuna cewa ma'aikatan sun fara rashin lafiya tsakanin ranar 4 zuwa 6 ga watan Yuli, yayin da bincike ya tabbatar da cewa kwayar Plasmodium ce ta haddasa barkewar cutar.
CNN ta wallafa cewa wannan nau'in kwayar cutar na daga cikin mafi hadari da tsanani wajen haddasa zazzabin cizon sauro.
Ana ci gaba da bincike
Hukumar kula da lafiya ta birnin Frankfurt ce ke jagorantar binciken domin gano ko sauro guda ne ko kuma sauro fiye da daya suka ciji ma'aikatan.

Source: Getty Images
An kuma kafa tarkuna a wuraren filin jirgin saman domin kama sauro, yayin da ake gudanar da binciken kwayoyin halitta domin gano asalinsu da kuma yankin da suka fito.
Sai dai shugaban hukumar lafiya ta Frankfurt, Peter Tinnemann, ya ce akwai yiwuwar sauro da ake zargi ya riga ya mutu, yana mai jaddada cewa hadarin kamuwa da cutar ga sauran al'ummar yankin ba shi da yawa.
Malam Anchau ya rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa babban malamin addinin Musulunci, Malam Muhammadu Anchau, ya rasu a garin Jos bayan doguwar jinya.
Rahotanni sun nuna cewa fitaccen malamin addinin Musuluncin, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ne ya jagoranci yi wa Malam Muhammadu Anchau sallar jana'iza.
Rasuwar malamin ta jefa almajiransa da sauran al'ummar Musulmi cikin jimami, inda mutane da dama suka yi ta aika sakonnin addu'ar neman gafara da rahama a gare shi.
Asali: Legit.ng

