Ranar zazzabin cizon sauro ta duniya: Hanyoyi uku mafi inganci domin kariya daga cutar
-Akwai sauran rina a kaba, duk da tarin kudin da ake kashewa wurin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a yankin Afrika har yanzu ba a ga bayanta ba.
-Cutar zazzabin cizon saura na kan gaba cikin cututtuka da suka kashe mutane a duniya
Zancen da ya fito daga kungiyar lafiya ta duniya (WHO) kimanin mutum 435,000 cutar zazzabin cizon sauron ke kashewa duk shekara. Akasarinsu ‘yan Afrika ne yayinda kashi 61 cikin dari nasu yarane ‘yan kasa da shekara 5.
Kwayar cuta mai suna Plasmodium ita ke haifar da wannan rashin lafiya, yayinda idan har bata samu kulawa ba zata iya haifar da wasu matsaloli kamar wahalar yin numfashi, tabuwar hanta da koda kai harma da sashen garkuwar jiki.
KU KARANTA:Shugaba Muhammadu Buhari ya bude Makaranta da gidaje a Jihar Borno
Duk da tarin kudaden da kasashe masu fama da cutar tare da WHO ke kashewa, har wa yau cutar na cigaba da yaduwa. Kudin da ya kai $3,1000,000 a iya cewa bai kawo karshe matsalar zazzabin cizon sauran ba.
Akwai wasu hanyoyi da yakamata duk wani dan Najeriya ko kuma sauran kasashen Afrika dake fama da cutar yayi amfani da su domin magance matsalar.
Na farko: Kariya daga cizon sauro, zaiyi matukar wahala ace an tsira daga cizon sauro musamman a kasashen dake da sauron mai yawan gaske. Hakan zai iya samuwa ta hanyar amfani da raga wacce aka sanya maganin kashe sauro.
Abu na biyu: Amfani da magunguna suka shafi rigakafi, mutum zai iya zuwa wurin likita domin shawara kan yanda zai kare kansa daga cutar zazazzabin cizon saura. Akwai wani mannshafawa a jiki wanda sauro bai kaunar warinsa akan iya amfani dashi.
Na uku: Tsaftace muhalli, sauro dai yana rayuwane a wuri maras tsafta don haka ya zama wajibi a garemu domin kariya ga cutar zazzabin cizon sauro ya kasance mun tsaftace muhallinmu ba tare da barin shi cikin dauda ba.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng