Zazzabin cizon sauro yana kashe yan Najeriya 9 a kowane minti 60, Minista

Zazzabin cizon sauro yana kashe yan Najeriya 9 a kowane minti 60, Minista

  • Ministan Lafiya, Osagie Ohanire, ya bayyana cewa yan Najeriya 9 na rasa ransu a kowane minti 60 saboda Malaria
  • Ministan ya koka kan yadda mutane suke mutuwa a faɗin kasa yayin wata ziyara da ma'ikatar lafiya ta kai Ogun
  • Ohanire ya ƙara cewa Najeriya ce gaba-gaba a kamuwa da zazzaɓin cizon sauro a faɗin duniya

Ogun - Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya koka kan yadda ake samun karuwar mace-mace da ciwon dake da alaƙa da zazzabin cizon sauro a faɗin kasar nan.

Dailytrust ta ruwaito ministan ya kara da cewa yan Najeriya 9 ne suke mutuwa da ciwon a kowace awa ɗaya.

Ehanire ya bayyana hakane ranar Litinin a Abeokuta, yayin da tawagar ma'aikatar lafiya da kuma kungiyar taimakon lafiya (SFH) suka ziyarci mataimakiyar gwamnan Ogun, Mrs. Noimot Salako-Oyedele.

Wata yar Najeriya na jinyar ɗiyarta dake ɗauke da Malaria
Zazzabin cizon sauro yana kashe yan Najeriya 9 a kowane minti 60, Minista Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Menene dalilin wannan ziyara?

Tawagar ma'aikatar lafiya da kungiyar SFH sun ziyarci mataimakiyar gwamnan ne domin neman goyon bayan gwamnati kan yaki da cutar zazzabin cizon sauro.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Attajirin Dan Kasuwa, Okunbo, Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Shugaba Buhari Ya Yi Jimami

Ehanire wanda ya samu wakilcin Timi Obot, ya koka kan cewa a duk mutum hudu da suka kamu da Malaria a duniya ɗaya ɗan Najeriya ne.

Ministan yace:

"Ya zama wajibi mu tashi tsaye domin magance yawaitar kisan da cutar Malaria take yi a faɗin ƙasar nan."
"Gwamnatin tarayya tare da haɗin guiwar SFH da shirin yaki da cutar Malaria ta ƙasa (NIMET) zasu raba ragar sauro miliyan 3.7m ga magidanta a faɗin kananan hukumomi 20 dake faɗin jihar."

Najeriya ce gaba-gaba a yawan Malaria a duniya

Da yake tsokaci kan rahoton duniya na 2010, Ministan yace Najeriya ce gaba-gaba inda take da kashi 27 na masu ɗauke da Malaria da kashi 23 da waɗanda suke mutuwa.

A jawabinta, mataimakiyar gwamnan tace gwamnati zata bada dukkanin goyon bayan da ake bukata don kammala rarraba ragar sauron cikin nasara.

Ta kara da cewa ragar tana taimkawa mutane matuka wajen rage kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro da wasu cututtuka.

Kara karanta wannan

Cuta Ta Barke a Jihar Katsina Ta Hallaka Akalla Mutum 60 Wasu 1,400 Sun Kamu

A wani labarin kuma shugaban rundunar sojojin kasa ya gargaɗi yan ta'addan kasar nan su tuba su mika makamansu

COAS Yahaya ya yi wannan kiran ne ranar Litinin a Maiduguri, jihar Borno yayin kaddamar da sabon shirin kula da jin dadin jami'an tsaro na haɗakar Operation Haɗin Kai.

Da yake jawabi a wurin taron manjo Yahaya yace duk waɗanda suka ki mika makamansu zasu fuskanci fushin sojoji domin zasu iso garesu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262