Jerin muhimman kalmomin hausa 20 da ma'anar su a harshen turanci

Jerin muhimman kalmomin hausa 20 da ma'anar su a harshen turanci

Shin kun san sunayen ababen nan a harshen turanci kuwa? Da yawan mu mun tsammaci wasu ababen da mu ke amfani da su a gargajiyance ko a Kasar nan ta mu, sun kebanta gare mu ne kadai.

Mai yiwuwa wasun mu su yi tsammanin ababe irin su gwate, dambu, dinya da dai sauran su, ba su da sunaye a harshen turanci.

To albashirinku, turawa da wasu launin bil'adama su na amfani da wadansu daga cikin su ko makamantan su.

Hakan yasa Legit.ng ta kawo muku jerin sunayen wasu ababen da mu ka sani da sunayen su a turance kamar haka:

1) Tsamiyar Biri - Black Velvet Tamarind

2) Agwaluma - African Star Apple

3) Giginya - Deleb Palm

4) Kainuwa - Water Lettuce

5) Mummuki - Bread

6) Laulawa - Bicycle

7) Kanya - Ebony Tree

8) Dumame - Recheuffe

KU KARANTA: Za'a fara gabatar da wani kayattacen wasan kwaikwayo kan yaki da rashawa cikin harshen hausa

9) Dambu - Chicoins

10) Gujiya - Bambara Nut

11) Magarya - Jujube

12) Rama - Jute

13) Rumbu - Silos

14) Lauje - Sickle

15) Masoro - West African Pepper

16) Gwaza - Cocoyam

17) Kyarkeci - Wolf

18) Beguwa - Porcupine

19) Sulke - Armour

20) Angurya - Cotton Seed

21) Gwate - Porridge

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel