Sai bayan bakka ake: Kalli yadda yaron Umar Musa Yar’adua ya tuna da mahaifinsa bayan shekara 10

Sai bayan bakka ake: Kalli yadda yaron Umar Musa Yar’adua ya tuna da mahaifinsa bayan shekara 10

Dan tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa Yar’adua, Musa ya tuna da mahaifinsa bayan shekaru 10 da rasuwa, inda ya yi masa wasu addu’o’i guda biyu daga cikin Al-Qur’ani.

A ranar 5 ga watan Mayun shekarar 2010 ne Yar’adua ya rasu bayan fama da matsananciyar rashin lafiya, koda yake dai kafin nan ya sha fama da ciwo, inda yayi jinya a kasar Saudiyya.

KU KARANTA: Gwamnan Katsina ya bayyana abin da yasa gwamnati ta garkame fadar masarautar Daura

Biyo bayan rasuwar sa a wani halin sarkakiya ne mataimakin, Goodluck Ebele Jonathan ya dare madafan iko, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ta tanada.

Punch ta ruwaito Musa ya tuna da mahaifin nasa ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Twitter a ranar Talata, inda yayi masa addu’o’i kamar haka;

“Ya Ubangiji, ba ka halicci wadannan haka nan ba, tsarki ya tabbata a gareka, Ka kare mu daga zabar wuta.” Surah ta 3, aya ta 191 na cikin Al-Qur’ani.

“Ya Ubangiji ka gafarta mana, ka dauke mana kurakuranmu, kuma Ka sa mu mutu tare da mutanen kirki.” Surah ta 3, aya ta 193 na cikin Al-Qur’ani.

A wani labari kuma, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya jinjinawa marigayi tsohon shugaban kasa Umar Musa Yar’adu, shekaru goma bayan mutuwarsa.

Goodluck ya wallafa sakon jinjinawar ne a shafnsa na Facebook, inda ya bayyana cewa Yar’Adua ya yi rayuwa sannan ya mutu wajen yi wa kasarsa hidima.

"Zan ci gaba da tuna Yar’Adua a matsayinsa na abokin aiki kuma ubangida wanda ya zama dan’uwana kuma aboki." Inji shi.

Bugu da kari yan Najeriya sun bayyana wasu muhimman abubuwa da suke tunawa da marigayi tsohon shugaban kasa Yar’adua dasu kamar haka;

- Biyan jahar Legas bashin kudin da take bin gwamnatin tarayya

- Kafa hukumar kula da tsagerun Nejda Delta

- Sanar da kadarorinsa da dukiyarsa ga yan Najeriya

- Kyakkyawar alaka tsakaninsa da yan majalisu

- Kafa kwamitin garambawul ga dokokin zaben Najeriya

- Aikin yashe kogin Neja

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel