Sojoji Sun Saka Yan Ta’adda cikin Rudani, Sun Yi Ajalin Babban Kwamandan ISWAP

Sojoji Sun Saka Yan Ta’adda cikin Rudani, Sun Yi Ajalin Babban Kwamandan ISWAP

  • Rashin wani babban kwamandan ISWAP, ya jefa shugabannin ƙungiyar cikin fargaba bayan Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kashe shi
  • Majiyoyin leƙen asiri sun ce an kashe kwamandan ne yayin da yake kan babur kusa da maboyar ’yan ta’addan Gargash
  • Lamarin ya sa ISWAP ta fara zargin akwai masu fallasa bayanan sirri, tare da nazarin hanyoyin sadarwa da motsin kwamandoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dikwa, Borno - An ce fargaba ta bazu tsakanin shugabannin Islamic State West Africa Province (ISWAP), bayan kashe babban kwamandanta.

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kawar da wani babban kwamandan kungiyar ISWAP mai suna WAL-GEGE a jihar Borno.

Sojoji sun kashe babban kwanadan ISWAP
Dakarun rundunar sojojin Najeriya a bakin daga. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Majiyoyin leƙen asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa an kashe WAL-GEGE ne yayin da yake tafiya a kan babur a babbar hanya kusa da Markaz ɗin ’yan ta’addan, wanda ke kusa da maboyar Gargash.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi barin wuta kan yan ta'adda, miyagu da dama sun rasa rayukansu

Yadda aka kashe kwamandan ISWAP

An ce an kashe WAL-GEGE ne a wani samamen da Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kai a ƙarƙashin Operation HADIN KAI (OPHK), a yankin Gargash da ke ƙaramar hukumar Dikwa a Borno.

Majiyoyin sun ce an gudanar da harin ne a matsayin wani ɓangare na hare-haren sama da ake gudanarwa bisa bayanan sirri, domin tarwatsa zirga-zirga da tsarin shugabancin ’yan ISWAP da ke aiki a yankin Dikwa.

Rahotanni sun ce kashe kwamandan ya haifar da damuwa a cikin ƙungiyar ’yan ta’addan, musamman saboda an kashe shi ne yayin da yake wucewa ta wani yanki da ake ganin yana ƙarƙashin ikonsu.

Lamarin ya kuma jawo bincike a cikin gida tsakanin ’yan ISWAP, inda wasu mambobin ƙungiyar ke zargin wasu mutanen cikin ƙungiyar da fallasa wa sojoji bayanan sirri game da motsin kwamandan.

An yi ajalin kwamandan ISWAP
Taswirar jihar Borno da ke fama da matsalolin tsaro. Hoto: Legit.
Source: Original

Halin da yan ta'adda ke ciki a yanzu

Bayanan leƙen asirin sun nuna cewa ’yan ta’addan ISWAP sun ƙara nuna shakku kan yiwuwar samun masu fallasa bayanai a cikinsu.

Kara karanta wannan

FAAC ta cika aljihun gwamnatin Tinubu da jihohi, an raba abin da ba a taba samu ba

Rahotanni sun ce ƙungiyar na sake duba hanyoyin sadarwarta da kuma tsarin zirga-zirgar kwamandoji da mayakanta bayan harin.

Majiyoyin sun ce wannan ci gaba ya kuma sa ’yan ISWAP yin la’akari da takaita amfani da wayoyin hannu tsakanin kwamandojin filin daga da mayaka.

Hakan ya samo asali ne daga fargabar cewa za a iya gano motsinsu ta hanyar sadarwa ko wasu hanyoyin leƙen asiri.

Martanin ƙungiyar na nuna ƙarin matsin lamba da jami’an tsaron Najeriya ke yi mata, yayin da suke ƙara sa ido da kai hare-haren sama kan kwamandoji, hanyoyin samar da kayayyaki da maboyar ’yan ta’adda a yankin Tafkin Chadi.

Kashe WAL-GEGE na da muhimmanci musamman saboda rasa manyan kwamandojin filin daga na iya kawo cikas ga daidaita ayyukan mayaka, zirga-zirgar kayayyaki da shirya hare-hare.

Sojoji sun kashe yan ISWAP 8 a Borno

Mun ba ku labarin cewa sojojin Operation Hadin Kai sun kashe mayakan ISWAP guda takwas a wani samamen sama da suka kai yankin Timbuktu Triangle, Borno.

Harin ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri kan ‘yan ta’addan da suka taru a Thethangala, suna shirin kai hari kan sojojin Najeriya.

Rundunar soji ta ce yanayin tsaro ya kasance cikin kwanciyar hankali amma babu tabbas, yayin da Operation Hadin Kai ke ci gaba da kai hare-hare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.