Shin da Gaske Gwamnatin Edo Ta Hana Davido Shiga Jihar bayan Kin ba Gwamna Hakuri
- Gwamnatin Jihar Edo ta yi magana kan rahoton cewa ta hana fitaccen mawakin Afrobeat, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, shiga jihar
- Kwamishinan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Kassim Afegbua, ya ce Edo gida ce ga kowa ba tare da la’akari da ra’ayinsa ko siyasarsa ba
- Gwamnatin ta ce za ta yi maraba da Davido kuma a shirye take ta haɗa gwiwa da shi idan ya shirya yin wasa a jihar nan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Edo - Gwamnatin Jihar Edo ta musanta cewa ta hana fitaccen mawakin Afrobeat, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, shiga jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa na jihar, Kassim Afegbua, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, 21 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan
Minista ya fasa kwai, an ji yadda ake shirin ƙarawa Atiku 'hawan jini' kafin zaben 2027

Source: Twitter
Gwamnatin Edo ta musanta haramcin
A cikin sanarwar, Afegbua ya ce gwamnatin jihar ba ta da hannu a irin wannan mataki, yana mai bayyana wanda ya sanar da haramcin a matsayin maƙiyin Jihar Edo da kuma mai yaudara, cewar rahoton The Punch.
"Maƙiyanmu sun sake farfaɗowa; ba mu hana Davido shiga Jihar Edo ba. Wanda ya sanar da wannan haramcin maƙiyin Jihar Edo ne, ɗan kwaikwayo kuma ɗan damfara."
“Gwamnatin Jihar Edo ta nesanta kanta daga irin wannan ɗabi’a ta ƙiyayya, kuma tana son ƙara bayyana cewa Jihar Edo gida ce ga kowa, ba tare da la’akari da imaninsa, ra’ayinsa na siyasa, kusancinsa da wata ƙungiya ko kuma alaƙarsa ta doka ba."
“A zahiri, idan Davido ya yi niyyar yin wasa a Jihar Edo nan gaba, jihar za ta kasance a shirye ta yi haɗin gwiwa da shi.”
Edo ta ce Davido ɗanta ne
Kwamishinan ya ce Gwamna Monday Okpebholo mutum ne da ke iya tafiyar da al’amura daidai da ra’ayoyi da rukunin jama’a daban-daban da ke jihar.
“Davido ɗaya ne daga cikin fitattun ’ya’yanmu, domin mahaifiyarsa ’yar asalin Jihar Edo ce. Shi abin koyi ne, kuma muna farin cikin kasancewa tare da shi."
“Idan yana son ziyartar Jihar Edo, za mu yi farin cikin tarbarsa da kuma shirya masa liyafa. Abin da ya faru a Jihar Osun sakamakon zaɓen makon da ya gabata siyasa ce kawai, ba wani abu na kashin kai ba. Babu wani abu na kashin kai a cikin maganganun da suka ƙara ƙaimin yakin neman zaɓen."
“Davido matashi ne da ya kasance ɗaya daga cikin jakadun Najeriya a duniya, yana ƙara wa ƙasar daraja tare da gina hanyoyin fahimtar juna tsakanin ɓangarorin siyasa da zamantakewa daban-daban.” In ji shi.

Source: Facebook
Afegbua ya ce gwamnatin jihar na farin ciki da yadda Davido ke gudanar da harkokinsa, da jajircewarsa da kuma yadda yake samun nasara a masana’antar waƙa.
"A matsayinta na gwamnati, muna farin ciki da ɗabi’arsa, jajircewarsa da kuma yadda yake samun nasara cikin tsari a masana’antar waƙa. A zahiri, muna masa fatan samun lambar yabo ta Grammy.” In ji shi.
Davido ya ki ba Gwamna Okpebholo hakuri
A wani labarin kuma, kun ji cewa David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya ce ba zai ba Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, hakuri ba.
Davido ya ce bai aikata wani abu mara kyau ba wajen wallafa sakamakon jarabawar WAEC na gwamnan.
Asali: Legit.ng

