“Kan Mijina Kato Ne Sosai”: Mata Mai Juna Biyu Ta Shiga Zullumi Yayin da Lokacin Nakudarta Ya Gabato

“Kan Mijina Kato Ne Sosai”: Mata Mai Juna Biyu Ta Shiga Zullumi Yayin da Lokacin Nakudarta Ya Gabato

  • Bidiyon wata matar aure dauke da juna biyu tana bai wa mata yan uwanta shawara kan irin mijin da za su aura ya yadu
  • A cikin bidiyon mai ban dariya, ta bukaci mata da su guji auren mazaje masu manyan kawuna domin su haihu cikin sauki
  • Bidiyonta ya haifar da martani daban-daban a tsakanin mata a sashinta sharhi a dandalin TikTok

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata mata mai juna biyu da ya tsufa sosai ta yi fice a dandalin TikTok bayan ta bai wa mata shawara mai ban dariya.

Matar mai juna biyu wacce aka kira da suna @omotarah5 a TikTok ta yada wani bidiyonta cikin tunani mai zurfi yayin da lokacin haihuwarta ke kara gabatowa.

Kara karanta wannan

"Ba su gane shi ba": Hamshakin mai kudi Femi Otedola ya shiga motar haya a wani tsohon bidiyo

Matar aure na zullumin nakuda
“Kan Mijina Kato Ne Sosai”: Mata Mai Juna Biyu Ta Shiga Zullumi Yayin da Lokacin Nakudarta Ya Gabato Hoto: @omotara5/TikTok.
Asali: TikTok

Mai ciki ta shawarci mata kan auren maza masu manyan kawuna

Omotarah ta shawarci mata da su duba girman kan abokan zamansu kafin su amsa masu da eh.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, ita bata duba girman kan mijinta ba kafin ta aure shi sannan yanzu tana fargabar cewa kan danta na iya zama kato wajen haifo shi.

Ta rubuta:

"Yayin da lokacin ya kusa kuma ka san cewa kan mijinka kato ne sosai. Yan mata ku duba kan abokan zamanku kafin ku ce eh."

Jama'a sun yi martani

Da suke martani a sashin sharhi, mata da dama sun ce suma sun auri mazaje masu manyan kawuna inda suka bayyana halin da suka riski kansu a dakin haihuwa.

Demzy ta ce:

"Ba ki yi la'akari da kan ba kafin ki aure shi."

@user6463421394383 ta ce:

Kara karanta wannan

Budurwa ta koka bayan ta ci karo da shinkafa a cikin cincin din 'mitifie' da ta siya a Legas

"Yar'uwata sai kin ga yadda suka yaga mun dukka bangarorin biyu kafin su fito."

@user8393545994452 ya yi martani:

"Ni ke da katon kai kuma yan mazana biyu suka dauko shi ba ga shege banza a dakin haihuwa."

DollyP_36 ta ce:

"Me yasa ba ku yi karin bayanin nan ba tun tuni na amsawa dan saurayina da eh kuma kansa kato ne fa."

Ayanfunke ta ce:

"Kenan muna da yawa da muka auri masu manyan kawuna chai."

Matar aure ta bankado sirrin mijinta

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata matar aure mai suna Onyinye Okoli, ta koka a soshiyal midiya bayan gano cewa mijinta na shekaru hudu ya haifi wani dan a waje.

Wata mai amfani da dandalin Facebook, Maria Ude Nwachi ce ta wallafa labarin kuma tuni ya haddasa cece-kuce a tsakanin jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel