Yanzu-yanzu: Mun gano ana shirin saka Bam lokacin Kirismeti, Hukumar DSS

Yanzu-yanzu: Mun gano ana shirin saka Bam lokacin Kirismeti, Hukumar DSS

- Ana shirin kai hari coci-coci lokacin bikin Kirismeti da sabuwar shekara

- Kakakin DSS, Afunanya, ya ankarar da yan Najeriya, musamman masu bukukuwa

- Ya bukaci yan Najeriya su nisanci taron jama'a musamman wannan lokacin

Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta gano wani shiri da wasu bata gari ke yi na sanya Bam a wuraren da ke da taron jama'a a fadin kasar lokacin bikin Kirismeti da sabon shekara.

A jawabin da kakakin hukumar, Peter Afunanya, ya saki ranar Talata, ya yi kira ga yan Najeriya su farga, kuma su fadawa jami'an tsaro duk wani abinda suka gani basu yarda da shi ba.

"Hukumar DSS na sanar da daukacin jama'a shirin da wasu batagari ke yi na kai hare-hare wuraren dake da taron jama'a wanda ya hada da manyan wurare lokacin hutun Kirismeti da sabon shekara," wani sashen jawbai yace.

"An yi shirin kai wadannan hare-hare ne ta hanyar amfani da bama-bamai, masu kunar bakin wake da kuma wasu makamai masu hadari."

"Manufar haka shine saka tsoro cikin zukatan mutane da kuma bata sunan gwamnati."

"Saboda haka, yan Najeriya su kasance cikin farga kuma su bada rahoton duk wani abin da suke zargi ga hukumomin tsaro."

Hukumar tana baiwa yan Najeriya tabbacin cewa tana hada kai da sauran hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyan al'umma.

KU KARANTA: Kada ku dogara da gwamnati don samun aiki, Ministan Buhari

Yanzu-yanzu: Mun gano ana shirin saka Bam lokacin Kirismeti, Hukumar DSS
Yanzu-yanzu: Mun gano ana shirin saka Bam lokacin Kirismeti, Hukumar DSS
Asali: Original

KU DUBA: Jihohi 3 da suka jefa Najeriya cikin halin Korona: Sakataren Gwamnatin Tarayya

A bangare guda, wani jami'in dan sanda kuma dogarin Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Pantami, ya shiga hannun masu garkuwa da mutane amma ya samu kubuta.

Dan sandan, wanda dan asalin jihar Nasarawa ne, yana kan hanyar zuwa Abuja daga Doma a karshen makon da ya gabata akayi garkuwa da shi a Ikari, wani kauye dake Gudi karkashin karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa.

Wani mai idon shaida ya ce wannan abu ya faru ne misalin karfe 8 na dare yayinda yan bindigan suka tare hanya, suka yi fashi, sannan sukayi awon gaba da mutane hudu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng