Tinubu zai Tura Kudi N75,000 ga 'Yan Najeriya Miliyan 70 domin Rage Talauci
- Gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shiryen raba N75,000 ga mutane miliyan 70 domin rage radadin wahalar rayuwa
- Hadimin shugaban kasa, Hon. Aliyu Audu ya bayyana cewa matakin yana cikin kudurin gwamnatin Tinubu na rage talauci
- Wani matashi mai sana'ar shayi ya bayyana wa Legit cewa tallafin zai rage wasu matsaloli amma ba lallai ya kai ga cire mutum a talauci ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta raba N75,000 ga mutane miliyan 70 a matsayin tallafi domin rage radadin rayuwa da jama’a ke fuskanta.
Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin kula da jama’a, Hon. Aliyu Audu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Hon. Aliyu Audu ya bayyana wasu nasarori da shugaba Bola Tinubu ya samu a watanni 19 da ya yi a kan karaga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu zai tura N750,000 ga 'yan Najeriya
A cewar Hon. Audu, matakin tura N75,000 na gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi daidai da kudurin ta na rage talauci a cikin kasa.
Ya ce, shugaban kasa Tinubu ya nuna gamsassun hujjoji na ci gaba a Najeriya a cikin watanni 19 kacal da ya kwashe yana kan karagar mulki.
“Wannan tallafin zai taimaka wajen rage radadin rayuwa, musamman ga talakawa, yayin da ake ci gaba da daukar matakan inganta tattalin arziki,”
- Hon. Aliyu Audu
Ya kara da cewa gwamnati na kan tafarki mai kyau wajen kyautata tsaro da kuma bunkasa harkokin noma domin rage farashin kayan abinci.
'Yan Najeriya da dama sun nuna na'am da shirin yayin da suke jiran karin bayani daga gwamnati kan fara tura kudin.
Tinubu ya habaka tattali inji Audu
Hon. Aliyu Audu ya bayyana cewa manufofin tattalin arziki da na kudi da gwamnatin Tinubu ta dauka sun haifar da karuwar kudi a asusun ajiyar kasashen wajen Najeriya.
Hadimin shugaban kasar ya ce gwamnati ta samu karin kusan $7.69m a cikin shekara guda a asusun ajiyarta na waje.
“Manufofin CBN kan sauye-sauyen tsarin kudin shiga sun karfafa asusun kasashen waje."
- Hon. Aliyu Audu
Gwamnatin ta kara da cewa bangaren tattali da ba shi da alaka da albarkatun mai da kuma karuwar samar da danyen mai sun kara wa gwamnatin tarayya kudin shiga.
A matakin jihohi da kananan hukumomi, Audu ya ce an samu karin kudin shiga daga asusun tarayya, wanda hakan ya ba su damar biyan bashin ‘yan kwangila tare da aiwatar wasu ayyuka
Tasirin manufofin gwamnati kan jama’a
Hon. Aliyu Audu ya yi bayanin cewa gwamnati ta dauki matakai masu karfi da suka inganta harkokin noma da tsaro, wanda hakan ke haifar da saukin kayan abinci.
The Guardian ta wallafa cewa an samu gagarumin ci gaba wajen biyan bashin kasa domin tabbatar da mutuncin Najeriya a idon duniya.
Ya kara da cewa kokarin da ake yi a bangaren tattalin arziki ya nuna cewa Najeriya za ta iya zama jagora wajen ci gaba a fannin kasuwanci da zuba jari.
Legit ta tattauna da mai shayi
Wani mai sana'ar shayi da taliyar indomi, Muhammad Ahmad ya zantawa Legit cewa mutane na bukatar tallafi amma ya kasance kudin na da kauri ta yadda za su iya mayar da shi jari.
"Da kamar yadda lamura suke a baya ne, da N75,000 kudi ne mai yawa. Amma a yanzu ko sana'ar shayi ba za ka iya farawa da kudin ba."
'Kamata ya yi a bayar da kudin da akalla za a iya amfani da shi wajen fara sana'a domin samun hanyar dogaro da kai, domin a haka ne kawai za a cire mutane daga talauci."
- Muhammad Ahmad
Dalilin karin kudin mai a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi bayani kan dalilin samun tashin farashin man fetur a watan Janairu.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin ta ce ba ta da hannu a harkokin da suka shafi farashin man fetur, za a sayar da mai ne yadda kasuwa ta zo da shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng