Wata sabuwa: Ana zaman dar-dar tsakanin al'ummar Tiv da Hausawa a garin Makurdi

Wata sabuwa: Ana zaman dar-dar tsakanin al'ummar Tiv da Hausawa a garin Makurdi

Kamar yadda muka samu daga majiyar mu, yanzu haka ana zaman dar-dar a garin Makurdi, babban birnin jihar Benuwe dake a shiyyar Arewa ta tsakiya a tsakanin al'ummomin yankin da suka hada da yan kabilar Tiv da kuma Hausawa.

Mun samu dai cewa hakan ya biyo bayan wasu bayanai na jita-jita da ake ta yadawa na cewa makiyaya a jihar za su kai hare-haren ta'addanci a garin biyo bayan kisan wasu Hausawa da 'yan Tiv din suka yi a karshen satin da ya gabata.

Wata sabuwa: Ana zaman dar-dar tsakanin al'ummar Tiv da Hausawa a garin Makurdi
Wata sabuwa: Ana zaman dar-dar tsakanin al'ummar Tiv da Hausawa a garin Makurdi

KU KARANTA: Kiristoci na shirin yin zanga-zangar kin jinin Buhari

Legit.ng ta samu cewa sakamakon haka ne ma tun jiya ba'a bude shaguna da makarantu ba domin gudun abun da ka iya zuwa ya dawo.

A wani labarin kuma, Kungiyar kiristoci ta Najeriya baki daya ta sanar da kudurin ta na gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadin su ga gwamnatin tarayyar Najeriya game da cigaban aukuwar hare-haren makiyaya a wuraren ibadar su ranar Lahadi mai zuwa.

Kamar dai yadda muka samu, kungiyar yanzu haka tana ta kara sanar da mabiya addinai a dukkan majami'un kasar nan da ma sauran masu fada aji da su fito kwansu-da-kwalkwata domin gudanar da zanga-zangar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel