Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya na shirin diban ma’aikatan noma 75,000

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya na shirin diban ma’aikatan noma 75,000

- Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za ta dauki ma’aikatan noma 75,000 domin karfafawa manoma gwiwa wajen samar da kayayyakin amfani

- Gwamnatin ta kuma kaddamar da kungiyar kifi na Najeriya tare da kudirin habbaka harkar kifi na gida biyo bayan rufe iyakokin Najeriya don hana shigo da kifi da sauran kayayyakin amfani daga kasashe waje

- Karamin ministan noma, Mustapha Shehuri ya ce FMARD ta jajirce don ganin ta samo mafita ga dukkanin kalubalen da ma’aikatar noma ke fuskanta bisa ga goyon bayan da ta samu daga shugaban kasa

Gwamnatin tarayya a ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamba, ta sanar da cewa za ta dauki ma’aikatan noma 75,000 domin karfafawa manoma gwiwa wajen samar da kayayyakin amfani.

Ta kuma kaddamar da kungiyar kifi na Najeriya tare da kudirin habbaka harkar kifi na gida biyo bayan rufe iyakokin Najeriya don hana shigo da kifi da sauransu.

Karamin ministan noma da cigaban karkara, Mustapha Shehuri, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin diban ma’aikata 75,000 a Maiduguri, jihar Borno, a lokacin ziyarar gani da ido a gine-ginen ma’aikatar gona da cigaban karkara na gwamnatin tarayya a arewa masu gabas.

Shehuri ya ce FMARD ta jajirce don ganin ta samo mafita ga dukkanin kalubalen da ma’aikatar noma ke fuskanta bisa ga goyon bayan da ta samu daga shugaban kasa.

KU KARATA KUMA: Zaben Kogi: Akwai wani makirci da ake kullawa na dage zabe – PDP ta yi zargi

Ya bayyana cewa duk da matsalolin tsaro, lokaci mai kyawu na dawowa kadan-kadan sannan zuwa yanzu, sama da kaso 60 na matasan Najeriya sun fada harkar noma.

A wai labari kuma, mun ji cewa Ministar kudi, kasafin kudi da tsare tsare, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatarta za ta fitar da makudan kudi naira biliyan 900 domin gudanar da manyan ayyuka.

Rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana cewa Ministar ta bayyana haka ne a ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamba yayin da take ganawa da manema labaru bayan kammala taron majalisar zartarwar Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel