An Ga Tashin Hankali a Amurka da Aka Kashe Mataimakiyar Babban Banki
- Erin Piacenti, mataimakiyar shugaban Bank of America mai shekaru 32, ta mutu bayan wata mata ta caka mata wuka a Times Square
- Wata mata mai shekaru 49 mai suna Pamela Cisneros ta kuma caka wa wani mutum mai shekaru 68 wuka, wanda ke asibiti cikin mawuyacin hali
- ‘Yan sanda sun harbe Cisneros bayan ta ƙi ajiye wuƙaƙen da ke hannunta tare da garzayawa zuwa kansu, daga bisani aka tabbatar da mutuwarta a asibiti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
New York, Amurka - Erin Piacenti, mataimakiyar shugaban Bank of America, ta mutu bayan wata mata ta caka mata wuka a harin da ya faru a Times Square da ke birnin New York.
Harin ya faru ne a yammacin Litinin, 31 ga watan Agustan 2026 inda wata mata da ke ɗauke da wuƙaƙe ta kai wa mutane biyu hari cikin tazarar kusan daƙiƙu 20.

Source: Twitter
Shafin Americanbanker ya ce 'yan sandan New York sun ce wanda aka fara kai wa hari wani mutum ne mai shekaru 68, wanda aka caka wa wuƙa a gefen dama na cikinsa.
‘Yan sanda sun bayyana yadda harin ya faru
Kwamishiniyar ‘yan sandan New York, Jessica Tisch, ta bayyana harin a matsayin wanda aka kai ba tare da wani dalili da aka sani ba.
Tisch ta ce wani shaida da ke wurin ya gaya wa masu bincike cewa ya ga wadda ake zargi ta ciro wuƙaƙe biyu daga cikin wata jaka kafin ta nufi wanda aka fara kai wa hari.
Ta ce matar ta daga wuƙaƙen kafin ta caka wa mutumin mai shekaru 68 a gefen dama na cikinsa.
Bayan haka, wadda ake zargin ta ci gaba da tafiya ta Seventh Avenue zuwa 42nd Street, inda ta kai hari kan Piacenti, mai shekaru 32. Piacenti ta samu raunuka sakamakon harin, kuma daga bisani ta mutu a asibiti.
An harbe wadda ake zargi
‘Yan sanda sun bayyana wadda ake zargin da sunan Pamela Cisneros, mai shekaru 49. Rahoton ya ce jami’an ‘yan sanda sun harbe Cisneros ne bayan ta ƙi ajiye makaman da ke hannunta tare da garzayawa zuwa gare su.
Daga bisani an kai ta asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarta, jaridar TheCable ta dauko labarin.
A halin yanzu, mutumin mai shekaru 68 da aka fara caka wa wuka yana kwance a asibiti, kuma ‘yan sanda sun ce yana cikin yanayi mai kyau.
Bank of America ya yi alhinin rasuwar Piacenti
Bank of America ya bayyana cewa ta shiga cikin jimami tare da kaduwa matuƙa sakamakon mutuwar Piacenti.
Bankin ya ce Piacenti ƙwararriyar ma’aikaciya ce kuma abokiyar aiki da ake matuƙar darajawa, wadda za a yi kewarta sosai.
‘Yan sanda na ci gaba da bincike domin gano cikakken abin da ya haddasa harin.

Source: Twitter
Iran ta kashe sojojin Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya kan sansanonin sojojin Amurka a Jordan, Kuwait da Bahrain.
Rundunar IRGC ta kuma yi zargin cewa mayakanta sun banka wa wuraren ajiyar man fetur na sansanin wuta tare da kashe wasu daga cikin sojojin Amurka.
Asali: Legit.ng

