"Kisan Rashin Imani," Magidanci Ya Halaka Matarsa Mai Tsohon Ciki a Jihar Neja

"Kisan Rashin Imani," Magidanci Ya Halaka Matarsa Mai Tsohon Ciki a Jihar Neja

  • An kama wani magidanci, Mohammed Sani bisa zargin halaka matarsa ta hanyar duka a Minna, jihar Neja
  • Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya ce sun samu labarin aika-aikar da magidancin ya yi kuma tuni aka kama shi
  • An ruwaito cewa Mohammed yana yawan samun saɓani da matarsa, Hauwa a cikin gidansu da ke Unguwar Bani Hashim Quaters

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Wani magidanci ɗan kimanin shekara 31, Mohammed Sani ya yi ajalin matarsa mai suna Hauwa a jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a Unguwar Bani Hashim Estate da ke Minna, babban birnin jihar Neja.

Magidanci ya kashe matarsa a Neja.
An kama wani mutumi da ake zargi da kisan matarsa a jihar Neja Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ƴan sanda sun kama mutumin da ake zargi domin gudanar da bincike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda miji ya kashe matarsa da tsohon ciki

An ruwaito cewa ma’auratan suna yawan faɗace-faɗace a tsakaninsu a cikin gida, wanda daga karshe ya yi sanadin mutuwar Hauwa.

Wasu bayanai sun nuna cewa Hauwa na da juna biyu da ya kai watanni tara kafin wannan lamari mara daɗi ya faru.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Ƴan sanda sun kai ɗauki wurin kisan

SP Abiodun ya ce:

"A ranar 3 ga Yuni, 2025, da misalin karfe 10:30 na dare, mun samu kiran gaggawa cewa an ga Hauwa Isah mai shekaru 24 ƴar Unguwar Bani Hashimu Estate, Limawa ‘A’ Minna, kwance a kasa babu rai, ga jini na kwarara.
“Jami’an ‘yan sanda daga ofishin A Division da ke Minna, sun garzaya wurin, inda suka tarar da gawar matar a kasa.
"Daga nan suka ɗauke ta zuwa Asibitin Gwamnati na Minna, inda likitoci suka tabbatar da cewa ta mutu. Haka kuma, an tabbatar da cewa tana dauke da ciki na wata tara."

Yan sanda sun kama wanda ya kashe matarsa a Neja.
Makwafta sun ba da shaida kan wanda ake zargi da kisan matarsa a Neja Hoto: @PoliceNG
Asali: Getty Images

Wanda ake zargi ya shiga hannun hukuma

Bisa bayanan da aka samu daga maƙwafta, kakakin ƴan sanda ya ce ana zargin mijinta, Mohammed Sani da hannu a mutuwar Hauwa, rahoton Premium Times.

"Ana zargin mijinta da aikata wannan aika-aikar bisa ga bayanan da makwabta suka bayar dangane da yawan cin zarafin matar da dukanta da yake yi.
"Yanzu haka an kama shi, kuma an mika lamarin ga sashen binciken manyan laifuka watau SCID a Minna," in ji shi.

Lamarin ya tayar da hankula, musamman duba da cewa mamaciyar tana dab da haihuwa kafin mutuwar da ta faru cikin yanayi na tashin hankali.

Kishi ya kai matan aure 2 gadon asibiti

A wani labarin, kun ji cewa wasu matan aure biyu sun jefa kansu a matsala, an kai su asibiti sakamakon shan maganin mata bayan mijinsu ya ƙara aure a Abuja.

Matan sun sha wani ruwan magani mai ƙarfi da aka sani da kayan mata domin ƙara ƙarfin sha’awa da nufin jan ra'ayin mijinsu a harkar kwanciya.

An ruwaito cewa tun farko matan sun yi haka ne bayan an ɗaura auren mijinsu da wata budurwa a matsayin matarsa ta uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262