Annoba Ta Bulla Legas, Ta Kama Sama da Mutum 400 Bayan Kashe Wasu da Dama

Annoba Ta Bulla Legas, Ta Kama Sama da Mutum 400 Bayan Kashe Wasu da Dama

  • An samu barkewar annobar kwalara a wasu kananan hukumomin jihar Legas da ke kudu maso yamman Najeriya
  • Gwamnatin jihar Legas ta ce annobar ta harbi mutane da dama kuma ta jawo asarar rayuka a ƙananan hukumomin jihar
  • Kananan hukumomin Lagos Island, Kosofo da Eti Osa suna cikin wuraren da aka fi samun yawaitar annobar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - An samu bullar cutar kwalara a wasu kananan hukumomi a jihar Legas da ke kudancin Najeriya.

Tun bayan bullar cutar an cigaba da samun karin adadin mutanen da suka mutu da wadanda suka kamu.

Jihar Legas
Kwalara ta kashe mutane da dama a Legas. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Leadership ta ruwaito mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin kiwon lafiya na karin haske kan lamarin.

Kara karanta wannan

Mutane kimanin 40 sun mutu, sama da 100 suna asibiti bayan sun yi tatul da giya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Illar da kwalara ta yi a Legas

Gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa a karon farko mutane 15 sun mutu sai aka kara samun mutane shida wanda a halin yanzu an samu adadin mutane 21 da cutar kwalara ta hallaka.

Sannan an samu mutane sama da 400 wadanda cutar ta kwantar a ƙananan hukumomi daban-daban kuma cutar na cigaba da yaɗuwa kamar wutar daji.

Meyasa kwalara ke yaɗuwa a Legas?

Mai ba gwamnan jihar shwarar kan harkokin kiwon lafiya, Dakta Kemi Ogunyemi ta ce an samu cakuduwar mutane daga wurare daban-daban a lokacin babbar sallah.

Mutanen kuma sun kara bazuwa cikin al'umma bayan hutun da gwamanti ta bayar ya kare, wanda suke dauke da cutar sai suka riƙa yaɗata da ga al'umma.

Kokarin da gwamnatin Legas take yi

Dakta Kemi Ogunyemi ta ce ma'aikatar lafiya da sauran ma'aikata suna ƙoƙarin shawo kan cutar, rahoton jaridar Premium Times.

Kara karanta wannan

Mahara sun dira Jihar Binuwai a babur, an shiga fargaba bayan kashe rayuka

Ta ce suna ƙoƙarin tattara samfurin ruwan sha, kayan abinci da kayan marmari domin gano daga inda annobar ta faro domin dakile ta.

Solomon Dalung ya caccaki Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ministan Buhari ya taso shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a gaba kan halin da ake ciki a ƙasar nan.

Solomon Dalung ya bayyana cewa kuskure ne babba ɗora alhakin halin da ƙasar nan ke ciki a kan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng