Barkewar cuta: Cutar kwalara ta barke a jihar Nasarawa, mutane 3 sun mutu, 121 sun kamu

Barkewar cuta: Cutar kwalara ta barke a jihar Nasarawa, mutane 3 sun mutu, 121 sun kamu

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, akalla mutane uku ne suka mutu sakamakon barkewar kwalara a jihar Nasarawa
  • A halin da ake ciki, an ce mutane 121 ne suke kwance a gadon asibiti inda suke fama da cutar ta kwalara
  • Hukumomi sun ba da shawarwari ga mazauna kan yadda za su kula da jiki da muhallansu duba da yawaitar kwalara

Nasarawa - Akalla mutane uku ne aka tabbatar sun mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a kananan hukumomin Awe da Obi na jihar Nasarawa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a Lafia, babban birnin jihar, Dakta Liman Mohammed, ya bayyana cewa a karamar hukumar Awe, an samu mutane 89 da suka kamu da cutar tare da mutuwar mutum daya.

Cutar kwalara ta barke a jihar Nasarawa, mutane 3 sun mutu, 121 sun kamu
Taswirar jihar Nasarawa | Hoto: channelstv.com
Source: UGC

Ya kuma bayyana cewa, a karamar hukumar Obi da ke jihar, akalla mutane biyu ne su ma suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar inda aka tabbatar kamuwar mutane 32.

Read also

Rahoto: Yadda aka hallaka mutane 52 a Sokoto cikin kwanaki biyu kacal

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mun samu rahoton mutuwa a karamar hukumar Awe da ta shafi wani yaro dan shekara shida wanda ya mutu cikin ‘yan sa’o’i kadan da isa cibiyar kiwon lafiya.
“Haka kuma a karamar hukumar Obi da ke jihar, mun samu rahoton mutuwar mutane biyu sakamakon amai da gudawa wanda muka tabbatar da cewa kwalara ce.”

Daily Trust ta ruwaito cewa, bayan tawagar ta ziyarci cibiyoyin lafiya a kananan hukumomin Awe da Obi, Dr Mohammed ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dauki tsauraran matakai ta hanyar samar da magunguna da sauran su, da nufin shawo kan lamarin.

Dokta Mohammed ya bayyana cewa manyan abubuwan da ke haifar da wannan matsalar sun hada da zubar da najasa sakaka da rashin tsaftar jiki da ta muhalli, ya kara da cewa batutuwan na iya zama ta sanadiyyar rashin wadataccen ruwan sha a yankin.

Read also

Babu unguwar da babu yan kwaya a Najeriya, Janar Buba Marwa

Yayin da yake danganta lamarin da halayen tsafta, Dokta Mohammed ya karfafa wa mutanen yankunan da abin ya shafa kwarin gwiwa da su guji yin bahaya a fili tare da kula da kyawawan dabi'un tsaftan muhalli don dakile matsalar.

A ci gaba da daukar matakan rigakafin da gwamnatin jihar ta dauka domin kaucewa afkuwar barkewar cutar kwalara da sauran cututtuka, Dakta Mohammed da tawagarsa sun kai ziyarar ga mai martaba Sarkin Awe Alhaji Isa Abubakar-Umar II.

Hakazalika sun gana da Osuko na Obi, Alhaji Aliyu Dangiwa Ogiri-Orume, inda suka bukaci ma’aikatan kiwon lafiya na al’umma da muhalli da su zage damtse wajen gudanar da ayyukansu a matakin farko.

A cikin 'yan watanni jaridar Vanguard ta ce, akalla mutane sama da 159 ne suka mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a jihohin Neja da Nasarawa.

Mutum 5 'yan rakiyar gawar wanda kwalara ta kashe sun mutu a hanyar kai gawa

Read also

Labari da Hotuna: Gini ya sake kifewa kan mutane a Jihar Legas, Jami'ai sun fara aikin ceto

A wani labarin, mutane biyar sun mutu yayin kai gawar dan uwansu da ya mutu sakamakon cutar kwalara a jihar Legas wanda suka dauko don kai shi gida jihar Sokoto.

Wadanda suka mutu an ruwaito cewa 'yan ci rani ne da ke zuwa jihar Legas.

Daily Trust ta ruwatio cewa suna zaune ne a Ojota, yankin da aka ce ya fi fama da cutar kwalara a jihar Legas.

An bayyana cewa daya daga cikinsu ya kamu da cutar kuma ya mutu jim kadan bayan kamuwarsa.

Source: Legit.ng

Online view pixel